Imam Ali a mahangar Muslunci: Sunnar Sa ya kamata a koya, ba Shi ya koyi ta wani ba !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Umarni ne na Annabi (S. A. W. W) cewa ya hore mu da bin sunnarsa da kuma sunnar Khalifofinsa shiryayyu masu shiryarwa, kuma riqo da wannan sunnah ita ce mafita da tsira ga al'umma. 


Sai dai kuma an sami sabani kan cewa suwanene wadannan shiryayyu masu shiryarwa, domin wasu sun tafi kan cewa hudu (4) ne, wasu kuma suka tafi kan cewa goma sha biyu (12) ne. 


To, idan ka cire fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W) babu wani mutum wandanda za ace Imam Ali (A. S) yabi sunnarsa. Wannan kuwa shine dalilin da yasa Imam (A. S) ya qi karbar sharadi na cewa sai ya bi sunnar Abubakar da Umar sannan a ba shi Khalifanci. 


Abinda nake son kawowa anan dai shine, wani matsayi wanda Imam Ali (A. S) ya kebanta dashi wanda hakan zai sa ya zama shine mafifici wanda zai iya zama abin koyi ga kowa bayan Annabi (S. A. W. W). 


Ya zo cikin wasu riwayoyi daga Manaqib nasa kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


علي بن أبي طالب في ميزان الإسلام 


(1)- أن رسول الله قال يوم خيبر: لأُعْطِيَنَّ هَذِهِ الرَّايَةَ رَجُلاً يَفْتَحُ اللَّهُ عَلَى يَدَيْهِ يُحِبُّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ، وَيُحِبَّهُ اللَّهُ وَرَسُولُهُ. قال: فبات الناس يدوكون ليلتهم أيهم يعطاها. قال: فلما أصبح الناس غدوا على رسول الله كلهم يرجون أن يعطاها، فقال: أَيْنَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ؟ فقالوا: هو يا رسول الله يشتكي عينيه. قال: فَأَرْسِلُوا إِلَيْهِ. فأتي به، فبصق رسول الله في عينيه، ودعا له فبرئ، حتى كأن لم يكن به وجع، فأعطاه الراية، فقال عليّ: يا رسول الله، أقاتلهم حتى يكونوا مثلنا؟ فقال: انْفُذْ عَلَى رِسْلِكَ حَتَّى تَنْزِلَ بِسَاحَتِهِمْ، ثُمَّ ادْعُهُمْ إِلَى الإِسْلاَمِ، وَأَخْبِرْهُمْ بِمَا يَجِبُ عَلَيْهِمْ مِنْ حَقِّ اللَّهِ فِيهِ، فَوَاللَّهِ لأَنْ يَهْدِي اللَّهُ بِكَ رَجُلاً وَاحِدًا خَيْرٌ لَكَ مِنْ أَنْ يَكُونَ لَكَ حُمْر النَّعَمِ."


Manzon Allah (S. A. W. W) ya fada ranar Khaibar; 


" ZAN BAYAR DA WANNAN TUTA GA WANI MUTUM WANDA ALLAH ZAI YI BUDI A HANNUNSA, YANA SON ALLAH DA MANZONSA, KUMA ALLAH NA SONSA DA MANZONSA. "


(Mai riwayar) Yace, sai mutane suka raya darensu kowannensu na tunanin wa za a bawa. Yace; " A yayin da mutane suka wayi gari sai suka yi sammako zuwa ga Manzon Allah (S. A. W. W) kowannensu na kwadayin a ba shi ita. Sai yace; 


" INA ALIYU BN ABIY 'DALIB ?"


Sai suka ce, " Yaa Ma'aikin Allah, ai yana fama da ciwon idanuwansa. " Yace; 


" KU AIKA GARE SHI . "


Aka zo da shi, sai Manzon Allah (S. A. Q. W) yaci tofi a idanuwan nasa, yayi masa addu'ah sai ya warke tamkar ma wani ciwo bai taba shafarsa ba. Sai ya ba shi Tura. Sai Aliyu yace; 


" YAA MA'AIKIN ALLAH! NA YAQE SU HAR SAI SUN KASANCE KAMAR MISALINMU (musulmai masu miqa wuya gare ka) ? Sai (Annabi) yace; 


" JEKA AKAN SHA'ANINKA (na jarunta wanda na sanka a kansa) HAR SAI KA SAUKA A FARFAJIYARSU, SANNAN KA KIRAYE SU ZUWA GA MUSLIMCI, KUMA KA BASU LABARI DA ABINDA YA WAJABA A KANSU NA DAGA HAQQIN ALLAH. NA RANTSE DA ALLAH, DA DAI ACE ALLAH ZAI SHIRYAR DA WANI MUTUM GUDA 'DAYA (1) TA HANYARKA YA FI AIKHAIRI GARE KA DA GARKEN JAJAYEN RAQUMA SU KASANCE GARE KA ."


Wannan hadisi na tabbatar mana ne cewa shi fa Imam Ali (A. S) na dabam ne cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W), domin shi kadai ne Annabi (S. A. W. W) ya fassara shi da cewa yana son Allah da Manzonsa, kuma shima Allah da Manzonsa na sonsa. 


Yanzu mai irin wannan matsayi za kayi tunanin akwai wani wanda ya fi shi wanda zai zama abin koyi gare shi cikin ayyukansa ?


(2)- وقد أعلى رسول الله مكانته، وقربه منه، حتى قال له لما استخلفه على المدينة في غزوة تبوك: أَلاَ تَرْضَى أَنْ تَكُونَ مِنِّي بِمَنْزِلَةِ هَارُونَ مِنْ مُوسَى؟ إِلاَّ أَنَّهُ لَيْسَ نَبِيُّ بَعْدِي.



Haqiqa Manzon Allah (S. A. W. W) ya daukaka matsayinsa, kuma ya kusanto dashi gare shi har yake fada masa yayin da ya Khalifantar da shi cikin Madinah a yaqin Tabuka :


" ASHE RANKA BAI YI DADI BA MATSAYINKA YA KASANCE A WAJENA KAMAR HARUNA DAGA MUSA BA ? SAI DAI KAWAI DON BABU WANI ANNABI A BAYANA ?"



(HAYATUS-SAHABA, MANAQIBU ALIYU BN ABIY 'DALIB)


Amma duk da wannan magana sai da aka qirqiro wasu maganganu na qarya don a lullube wannan daraja tasa. Aka kawo wani hadisi kamar haka; 


وقال الرسول : "لَوْ كَانَ نَبِيٌّ بَعْدِي لَكَانَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ"


الترمذي: 3619


Manzon Allah (S. A. W. W) yace; 


" DA ACE AKWAI WANI ANNABI A BAYANA DA UMAR NE ."


(Sahihu-Tirmidhi, hadisi mai lamba 3619)


Yanzu irin wannan maganganu da ake kawowa masu cin karo da juna ba za susa mu tashi muyi karatu da bincike na gaskiya don fayyace wadannan al'amra ba ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


      (08137925034)


2nd April, 2021/ 20th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post