Hijabi a Musulunci Kashi na Uku (III)




*SHIN ALLAH SUBHANAHU WATA ALLAH NE YA WAJABTA SANYA HIJABI A CIKIN QUR'ANI MAI TSARKI, SANNAN AKWAI HADISAN ANNABI (S) DA SUKA TABBATAR DA HAKA KO-KO DAI KITABUR-RA'ASI NE?*


*AMSA:*

Lallai Allah (SWT) madaukakin Sarki ne ya saukar da ayar sanya Hijabi ga matayen muminai ba KITABUR-RA'ASI ba ne, sannan HADISAN ANNABI (S) Dana A'IMMATUL-ISLAM (as) suma sunyi bayani akan HIJABI, amma bari mu dauki wata aya mai mahimmancin gaske wanda tana daga daya daga cikin ayoyin da sukai magana game HIJABI, idan muka duba sura ta 24, Suratun-Nur aya ta talatin da daya (31), za mu ga in da Allah Subhanahu wata Allah yake cewa Manzon Allah (SAWW).


"KA CE WA MUMINAI MATA SU SAUKE IDANUWANSU DAGA GANINSU, SANNAN KUMA SU TSARE AL'AURANSU, KUMA KADA SU BAYYANAR DA KWALLIYARSU, SAI DAI WANI BANGARE WANDA YAKE BAYYANAN NE GARE SU, KUMA SU SANYA MAYAFANSU AKANSU DA WUYAN RIGUNANSU".


SHARHI:

1=KACE WA MUMINAI MATA SU SAUKAR DA IDANUWANSU DAGA GANINSU.


Me Allah yake nufi da cewa: Kacewa Mumina mata su sauke idanuwansu daga ganinsu? 

Anan abin da ake nufi shine kada muminai mata suyi kwalliya wanda zai janyo hankalin maza, ko karkatar da hankalin maza zuwa gare su, ko kuma sabbaba wani abu dazai janyo hankalinsu har ya kai ga aikata haram! To wannan abun ko menene shi to shi ne ake magana akai, Ma'ana kada suyi ta yin kallo wanda ba kauda kai, wanda Hausawa suke kiransa da suna da kallon KURULLA, wato kallon KWAKWAF! Wanda zai jawo aikata sabon ALLAH, amma kallon da Shari'a ta yarda da shi shine, kallo wanda daka an kalla za'a saukar da idanuwa, ko kuma a kauda kai ba tare da an kirkiro abin da jawo aikata HARAM ba!


2= SANNAN KUMA SU TSARE AL'AURANSU.


 Shine kada su bayyanar da al'auransu ga wani namijin da baida ce ba, ma'ana su kiyaye kansu, da kawunansu, su kula da mutuncinsu ta kowacce fuska, da kulle duk wata kofa ta janyowa ko karfafawa, zuwa ga sabawa iyakokin Allah, ko yada FASADI adoran kasa ta hanyar bijirewa bin Ummarnin Allah, ba wanda Shari'a ta halartaba wajibi ne su kiyayesu ta kowanne irin yanayi da kuma ta kowacce fuska a gida ne ko a lokacin fitarsu ne.


3.= KUMA KADA SU BAYYANAR DA KWALLIYARSU,


In muka dauki kalmar ZEENA (KWALLIYA) cikin wannan aya mai girma wanda malamai sukai maganganu akanta ita ZEENA ta kasu gida biyu, akwai wanda Allah ya halicci mace da ita kamar yanayin jikinta da siffofin halittarta shi ma ZEENA ne, akwai kuma (ZEENA) wanda sanya ta akeyi kamar kunshi, zanen hannu, jan baki, lalle, da tafiyar KWALISA wanda zai janyo hankalin namiji, to duka wadannan Zinonin da mata suke sanyawa kada su bayyanar da wannan ZEENA din wato adonsu ga wanda bai dace ba, gaba daya wannan Zeenonin biyu da ta jikinsu wanda Allah ya halicce su da ita, da kuma wanda suke sanyawa wajan kwalliyarsu wajibi ne mace ta boye su ga dukkannin namijin da bai da ce ya gani ba, sai wanda Shari'a ta yarda, kuma ta amince da ita ya gani ga wanda yadace.


4= SAI DAI WANI BANGARE  WANDA YAKE BAYYANAN NE NE GARE SU. 


A wannan wurin na (ILLAH MA'AZAHARA MINHA), din nan malamai da yawa sunyi maganganu akai, akan cewa me nene ma (ILLAH MA'AZAHARA MINHA), amma yawancin su sun tafi akan cewa shi ne FUSKA da WUYAN HANNU shi ne mace bayan ta rufe dukkannin jikinta ba matsala don an gansu matukar ba kwalliya ko zane, ko ado wanda zai jawo hankalin maza su ganshi bayan sun rufe komai da komai nasu, ta yadda ba zai jawo hankalin namijin da bai da ce ya gani ba, shi ma SAYYID ALI KHAMNA'I (H) nazarinsa akan (ILLAH MA'AZAHARA MINHA), FUSKARSU da HANNAYEN matan ba Ishkhal don sun bayyana FUSKARSU da HANNAYE da dai sauran MARAJI'AI wanda suma suka tafi akan hakan.


Ya zo a cikin ruwaya cewa, wata rana ASMA'U kanwar UMMUL-MUNINA AISHA 'yar ABUBAKAR ta zo  gidan Annabin Rahama (s) wajan 'yar uwarta UMMUL-MIMINA AISHA, tana zuwa sai Manzon Rahama (s) ya yayi FUSKA ma'ana ya kauda fuskarsa mai tsarki gare ta, sai sukai mamaki, me ya sa haka? 

Sai Manzon Rahama (s) yake cewa, Ya ASMA'U idan mace ta kai shekarun BALAGHA bai da ce aga jikinta ba, sai dai FUSKA da WUYAN HANNAYENTA zuwa karshen ya tsunta na karshe. 


Wannan ruyawa ta zo ne acikin littafin SUNNAH DUR-RUL-MANSUR na IMAM SUYUDI, a karkashin Tafsirin wannan ayar da take magana akan HIJABI da kuma wurin da mata ya kamata a gani ba matsala.


Sannan ruwayoyi sunzo daga A'IMMATUL-ISLAM (AS) masu yawan gaske wanda suke nuni da cewa, ajikin mace abin za a iya gani ba ISHKHAL shi ne FUSKA da HANNUNTA.


Misali, idan muka dauki wannan ruwayan mai mahimmanci wanda aka ruwaito daga Mas'ada Bin Ziyada ya ce: Naji IMAM JA'AFAR (as) an tambaye shi abin da mace take bayyanarwa na adonta? 

Sai ya ce: FUSKA da HANNAYE.

Yanzu idan mukayi la'akari da wadannan Hadisai zamu fahimci ma'anar (ILLAH MA'AZAHARA MINHA), shi ne abin da Shari'a ta yarda ba matsala a gani ajikin mace FUSKA da HANNUNTA, yanzu idan mukalura wannan ayar da kuma Hadisi sun bayyana mana ma'anar (ILLAH MA'AZAHARA MINHA) bamuda ISHKHAL.


5= SANNAN KUMA SU SANYA MAYAFANSU AKANSU DA WUYAN RIGUNANSU.


Abin nufi anan shi ne su sanya mayafin da zai rufe musu kansu da wuyan rigunansu wannan ya nuna gaba dayan jiki ayar take nufi da dukkanin sassan jikin, tunda daka kansu da wuyansu da duk wani sassan jikinsu ya kasance ya rufu da kyau, wannan mayafi wanda muke kiransa da suna HIJABI ko SITRA wanda kaya ne da mata Muminai Musulmai suke sawa wanda Allah  ya wajabta musu domin cikar KAMALARSU, da kuma mutuncinsu.


TO, YANZU MUNSAN MA'ANAR HIJABI, MUNSAN KUMA DALILIN DA YASA MUKE SANYA HIJABI, TO WANE IRIN HIJABI MACE YA KAMATA TA SANYA?


AMSA:

Hijjabin da mace mumina ya kamata ta sanya shi ne:


1. Ya kasance Hijabin ba mai launin ado ba wanda zai iya jawo hankalin namiji zuwa gareataba.


2. Ya zama Hijabin ba mai kyal-kyali ba, ko duwatsu na ado masu kyalli akansa ba, ko rodi-rodin wani abu wanda zai janwo hankalin namijiba.


3. Ya zama Hijabin ba mai shara-shara ba, ko wanda za'a iya ganin wani abu ajikin mace ba.


4. Ya zama Hijabin bai kasance wanda zai iya matse jikin mace ba misali, kamar na ROBA.


5. Ya zama shi wannan mayafin wanda muke ce masa Hijabi ya kasance ba mara nauyi ba, wanda ISKA za ta iya daga shi ba idan an sanya shi ba.


6. Ya zama Shi HIJABIN ba dangalalle ba, wanda sai an sanya shi amma bai rufe wani sashi na mace ba, ya kasance wanda zai rufe dukkannin jikin mace da kyan gaske.


7. Sannan kuma mace mumina tana sanya HIJABI ne domin neman yardar Allah, da kusanci zuwa ga ALLAH (SWT) madaukakin SARKI, ba wai tana sa HIJABI ne amma kuma ba HADAFI mai bada sakamako zuwa ga Allah ba.


8. Ana sanya Hijabi ne ba don nagani a gidan mu ana sanya Hijabi ba.


9. Ana sanya Hijabi ne ba don na tashi na gani a gidanmu ana sanyawa ba.


10. Ana sanya Hijabi ne badon in na fita ba Hijabi ba za aita ce-ce-ku-ce-ce akaina ba, saboda an sanni ina sanyawa ba, ko don yayi ba.


11. Duka wadannan baya nai na sanya Hijabi da ake magana akansu, matan muminai QUR'ANI yake magana akansu, domin sune, za su bi umurnin Allah, kuma sune, za su sanya shi domin neman yardar Allah Subhanahu wata Allah, shi yasa QUR'ANI yai amfani da sunan mata muminai, domin mumini ne yake abu don Allah, ba don yabo ba, ba don ya burge ba, ba don yayi suna ba, ko akwai kowa, ko ba kowa, ko an sani, ko ba a sani ba, shi dai burinsa mumini yayi don Allah, Allah ya yarda da abun da yakeyi, ko-da-ko kowa yana inkarinsa. 


Duk da yake malamai da yawan gaske sunyi maganganu akan wane irin Hijabi mata muminai za su sanya, kowa ya kawo irin Nazariyya dinsa akan kalan Hijabin da za'a sanya, amma dai JAMHUUR din malamai sun tafi akan kalar baki yafi dacewa mace ta sanya, saboda shi ne duk cikin ka yayyakin da malamai sukayi muhawara akai yafi boye siffofin mace idan ta sanya shi, kuma shi ne baya bada kalar daukar hankali, kuma shi ne yafi kyawun SHAMAKI ga mace akan sauran. Wallahu ta'ala a'alam


*Binya Shi'a Kauran-Wali, Kudan*

*3th April, 2021*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post