Qalubale Gare ku Iyaye Mata !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SOYAYYAR IYAYE KUSANCI NE TSAKANIN 'YA'YA


Duk da cewa mafi yawan mata basu son zama da 'yar'uwa a matsayin abokiyar zama (kishiya), sai dai hakan bai hana mai gidansu qaro wata matar ba in har yana da buqatar hakan tare da iko. 


Wasu kan iya zama bisa lalura (dole) amma ba wai bisa son ransu ba, ko da kuwa babu wata fitina ta bangaren wacce aka kawo mata ko aka kawo musu. Cikin irin wannan zama na lalura ne sai kaga ko kaji ana samun sabani tsakaninsu wanda suna da ikon kaucewa wannan sabanin, amma saboda bin son zuciyarsu sai su riqa haifar da wata fitina a tsakaninsu. 


Ya zo cikin NAHJUL-BALAAGHA daga inda Imam Ali (A. S)  ke cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 نهج البلاغة قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع‏: " مَوَدَّةُ الْآبَاءِ قَرَابَةٌ بَيْنَ الْأَبْنَاءِ."


" SOYAYYAR MAHAIFA KUSANCI NE TSAKANIN 'YA'YA  ."


Abinda wannan hadisi ke koyar damu shine, idan ya kasance iyaye (Uwa da Uba) na nunawa junansu soyayya hakan zai qara kusanci tsakanin 'ya'yansu. 


Yadda za ku qara fahinta shine, idan ya kasance an sami mata biyu ko uku ko hudu qarqashin mutum daya (1), sai ya kasance suna nunawa junansu soyayya, kowacce na son 'yar'uwarta kuma suna kyautatawa juna tare da tausayin juna, to, hakan zai qara kusanci tsakanin 'ya'yansu, domin za su riqa gani daga iyayensu har suma su koya. 


Amma idan ya kasance saboda ba a son zaman tare a matsayin kishiyoyi sai ya zama ana muzantawa juna ta yadda 'ya'yansu za su fahinci haka, to, tabbas za a sami sabani tsakanin 'ya'yansu. Domin maimakon ace sun so juna tare da nuna cewa su abu guda ne, zai zama tasirin abinda suke gani daga iyayensu ya tasirantu cikinsu.


Ana nan wataran in da nisan kwana sai kaga babu zaman lafiya da qaunar juna a tsakanin 'ya'yan nasu , daga nan kuma iyayen suyi qoqarin gyarawa amma ba za suyi nasara ba tunda sun kaucewa hanyar tun farko. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


      (08137925034)


22nd March, 2021/  9th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post