Matsalolin Yin Aure a Cikin Watanni Biyu Kafin Azumi (Rajab Da Sha'aban) Kashi na uku !!!




FITA NA UKU(3) ! 


Bismihi ta'ala


A rubutuna na baya na fara bayani akan ababen da yin aure a wannan lokaci yake shafa ko haifarwa, insha Allah wannan zaya zama rubutu na karshe akan hakan, kuma zan cigaba ne daga na uku.


3_ GINUWAR TARBIYYAR ABINDA ZASU HAIFA : Ginuwar tarbiyya da tsara iyali yakan farane daga watannin farko na ma'aurata, hatta daga tsarin yadda zasu rika cin abinci, kalaci( breakfast), tashi daga bacci, da kuma mabanbantan ababe a wannan lokacin suke tsarawa. Yana tasirantar yaro ya tashi yaga yadda ake gudanar da rayuwa a gidansu, domin a dabi'a na dan Adam yana riko sosai da abinda ya rigada ya saba dashi, da wahalan gaske ka raba mutum da halin da ya rigada ya saba dashi.


Idan ba'a anfanu da wannan lokacin ba, ma'ana aka gudanar da ibadu cikin nutsuwa, zaya zamana Kafin wani watan irinsa ya dawo kunyi sabo da wasu dabi'un da bazaku iya bari ba, sannan munada sani cewa duk wanda aka daurawa aure Allah yana yafe masa zunubai da yawan gaske, wasu malamai ma sunce yakan koma kamar yau aka haifesa, saidai laifin bawa tsakaninsa da bawa dan uwansa, wanda wannan Allah baya yafesa sai idan wanda akayiwa din ya yafe, kenan zaya zama baku samu garabasar wannan lokaci ba, har kun sake tara wasu laifuka din, daga bakin ma'aurata da dama  sukan rasa damar tsarawa yaransu ababe masu kyau saboda a wannan lokacin hankalinsu na kan junansu ne da son biyawa juna bukatu, da lokacin ya wuce kuma an fara sabo da halin juna an kuma fara gajiya da juna sai ya zamana wata magana ake daban ba wannan ba, sai an haifa yaro sannan a fara tunani akansa. Bayan yanada kyau tun kafin a haifa yaro a tanadar masa abubuwan da zasu taimaka rayuwarsa duniya da lahira. Anfanin dake cikin wa'yannan watanni sun wuce musu basu saka yaransu dasu kansu aciki ba, wanda hatta da abinda akafi yawan aikatawa da cikin yaro to yakan iya tashi da wannan dabi'a din, idan mai kyau ne shikenan idan akasin hakan ne sai anyi fama dashi wurin gyarawa.


4_ HALASCI DA HARAMCI A TSAKANINSU : A wannan lokacin ba'a cika kula da harancin dake cikin auren ba ko Halasci, kawai ana kokarin kasancewa da juna ne, da gamsar da juna ta kowane fuska, shauki da sha'awan juna baya bari a kula da hakan. Wanda hakan ke saka a rika samun matsala da lokutan gudanar da ibadu na wajibi.


       Wannan har a sauran watanni ana samun irin haka, rashin kula da wa'yannan abubuwan, saboda so ya rufe musu ido, sai kaga gida ankai karfe 7, 7:30, har 8 wani lokacin ba'ayi asubah ba, bayan hakan zaya iya tasiri ga rayuwarsu gaba dayanta, amma ba'a kula da hakan.


MAFITA A ADDINI!!

 

Addinin musulunci shine addinin daya dace da rayuwar dan Adam ciki da wajenta. Tsira da aminicin Allah su tabba ga manzon daya kiyaye komai ya bayyana mana komai bai barmu da jahilcin komi ba.


Hankali shine babban makamin yaka da kuma Kare kai daga dukkan wani abinda akasin hankali zaya kawo. 


Ina mana fatan kiyaye dokokin Allah a ko'ina a kuma koda yaushe, Allah ya yafe mana kura kurenmu ya shirya mana zuri'armu, ya bamu ikon anfani da gaskiya ko daga bakin wa muka jita.


Nagode sosai da lokutanku masu daraja da kuka bani, ina neman afuwan Allah akan duk abinda na fada ba daidai ba, nagode.


✍🏽Zarah A Zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post