Maraba Da Zuwan Hujjar Allah A Doron Duniya Imam Mahadi (A.f) !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


YAU TAKE RANAR HAIHUWAR IMAM MAHDI (A. F) DA SAYYID ZAKZAKY (H)


A irin wannan rana ce 15th Sha'aban aka haifi Limamin qarshe cikin jerin Limaman shiriya goma sha biyu (12) wadanda Annabi (S. A. W. W) yabar mana kuma ya umarce mu kan cewa muyi riqo dasu a bayansa don kada mu halaka. 


Sannan a irin wannan ranar ce aka haifi mafi girma cikin mataimakansa (A. F), wato Sayyid Zakzaky (H).


       NASABARSA (A. F)


Shine Muhammad Bn Hassan Al-Khalis Bn Aliyu Al-Hadiy Bn Muhammad Jawwad Bn Aliyu Al-Ridha Bn Musal-Kazeem Bn Ja'afar As-Sadiq Bn Muhammad Baqir Bn Aliyu Zainul-Abideen Bn Hussaini Bn Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S)


Mahaifiyarsa kuwa ita ce Ummu-Walad, ana ce mata Narjis .


Al-Kunyarsa ana ce masa (Abu Qaseem), sannan kuma laqabunsa ana ce masa; -


Imamu bil-Hujja, 


Al-Mahdi, 


Al-Khalafus-Salih, 


Al-Qa'eem, 


Al-Muntazar,


Sahibuz-Zamaan.  Sai dai mafi shahara daga cikinsu shine Mahdi  (A. F). 


Haihuwarsa kuwa ta zo cikin riwaya kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼



 إكمال الدين ابْنُ عِصَامٍ عَنِ الْكُلَيْنِيِّ عَنْ عَلِيِّ بْنِ مُحَمَّدٍ قَالَ‏ وُلِدَ الصَّاحِبُ ع فِي النِّصْفِ مِنْ شَعْبَانَ سَنَةَ خَمْسٍ وَ خَمْسِينَ وَ مِائَتَيْنِ.


Ya zo cikin Ikhmaalud-Deen na Ibn Isaam daga Kulainiy daga Aliyu Bn Muhammad yace;  " AN HAIFI SAHIBUZ-ZAMAAN (A. S) CIKIN RABIN SHA'ABAN (15) A SHEKARA TA 255 ."


A wata riwaya kuma,


 عَنْ مُحَمَّدٍ الْعَطَّارِ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ النَّيْسَابُورِيِّ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ الْمُنْذِرِ عَنْ حَمْزَةَ بْنِ أَبِي الْفَتْحِ قَالَ: جَاءَنِي يَوْماً فَقَالَ لِي الْبِشَارَةَ وُلِدَ الْبَارِحَةَ فِي الدَّارِ مَوْلُودٌ لِأَبِي مُحَمَّدٍ ع وَ أَمَرَ بِكِتْمَانِهِ قُلْتُ وَ مَا اسْمُهُ قَالَ سُمِّيَ بِمُحَمَّدٍ وَ كُنِّيَ بِجَعْفَرٍ.


Daga Muhammad 'Daddariy, daga Hassan Bn Aliyu An-Naisaburiy, daga Hassan Bn Munziri, daga Hamzata Bn Abiy Fathi yace, " WATA RANA YA ZO MIN SAI YAYI MIN BUSHARA CEWA CIKIN DARE AN HAIFI WANI ABIN HAIHUWA CIKIN DARE GA BABAN MUHAMMAD, KUMA AKAYI UMARNI DA BOYE SHI. " NACE, TO, MENENE SUNANSA  ? YACE, 


" AN AMBACE SHI DA MUHAMMAD NE, SANNNA AKAYI MASA ALKUNYA  DA JA'AFAR. "


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏51، ص: 16


Siffarsa ko kakanninsa (A. F) ta zo cikin wani hadisi kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


عَنْ هِشَامِ بْنِ سَالِمٍ عَنْ زَيْدٍ الْكُنَاسِيِّ قَالَ سَمِعْتُ أَبَا جَعْفَرٍ مُحَمَّدَ بْنَ عَلِيٍّ الْبَاقِرَ ع يَقُولُ‏ إِنَّ صَاحِبَ هَذَا الْأَمْرِ فِيهِ شَبَهٌ مِنْ يُوسُفَ مِنْ أَمَةٍ سَوْدَاءَ يُصْلِحُ اللَّهُ لَهُ أَمْرَهُ فِي لَيْلَةٍ.


Daga Hishaam Bn Saalim, daga Zaid Al-Kunasiyyi yace, " Na ji baban Ja'afar Muhammad Bn Aliyu Al-Baqeer (A. S) yana cewa: " LALLE MA'ABOCIN WANNAN AL'AMARI YAYI KAMA DA YUSUF (A. S) NE TA BANGAREN MAHAIFIYA. BAQA CE, ALLAH ZAI KYAUTATA MASA AL'AMARINSA CIKIN DARE ."


Anan ana nufi ne mahaifiyarsa (A. F) baqar fata ce mutuniyar Africa kamar yadda mahaifiyar Annabi Yusuf (A. S) ta kasance ita ma baqar fata ce.


A halin yanzu Imam (A. F) na cikin Ghaibatul-Kubra wanda a halin yanzu sauraren bayyanarsa ake yi don kawar da zalunci da kuma shimfida adalci a doron qasa. 


       SAYYID ZAKZAKY (H)


Sayyid Zakzaky (H) shine babba cikin manyan mataimakan Imam Mahdi (A. F) wanda haihuwarsa tazo daidai da ranar haihuwar Limamin qarshe (A. F). 


An haifi Sayyid Zakzaky (H) ne a Unguwar Fada (wacce daga baya ta koma Kwarbai) cikin Birnin Zaria daidai ketowar Alfijri na ranar 15th ga Sha'aban a shekara ta 1372 bayan Hijra wanda yayi daidai da 12 ga watan Mayu (May) na shekarar 1953 (Miladiyya) na haihuwar Annabi Isah Al-Masihu (A. S). 


              NASABARSA (H) 


Mahaifinsa shine Malam Ya'aqub (wanda aka fi sani da Magaji), dan Aliyu dan Muhammad Tajuddeen dan Hussaini. 


Mahaifiyarsa (H) kuwa ita ce Hajiya Saliha (wacce aka fi sani da Hari) 'yar malam Jammo. 


Sayyid Zakzaky (H) ya taso cikin Birnin Zaria ne wanda mafi yawan karatukansa na addini yayi su ne cikin zaurukan manyan malamai dake garin. Kuma ya kasance mai aikata dukkan abinda ya kasance, shi yasa samartakarsa ta sama abin sha'awa kuma abin koyi ga al'ummar garin, musamman na unguwarsu da kuma wadanda yake mu'amala dasu.


Yayi karatun zamani a cikin garin Zaria da Kano,  sannan ya dawo cikin Birnin Zaria ya cigaba da karatunsa na zamani a Jami'ar Ahmadu Bello cikin shekara ta 1976/77,  sannan cikin wannan makarantar ne ya soma gwagwarmayar addinin muslimci yana dan shekara 25 a duniya. 


Ya hadu da jarrabawowi masu tsanani irin jarrabawowin da Allah ke yiwa bayinsa Annaba da Manzanni (A. S) dama sauran bayinSa salihai. 


Zuwa wannan lokaci da nake rubutun nan yana hannun azzalumar gwamnatin Fir'auna Buhari wanda yake tsare dashi tun watan 12 na shekarar 2015, kuma da iznin Allah muna kyautata zaton fitowarsa zuwa gare mu cikin izza nan ba da jimawa ba  !


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


28th March, 2021/ 15th Sha'aban, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post