Shahid Ishaq ka cika alqawari: Gudunmawar Shahid Ishaqa a wajen bada haqqin Shuhada'u


 

*Comrade Naziru sabaty gusau.✍🏻*


Dasunan Allah me rahama me jinqai.


Godiya ta tabbata ga ubangijin shahid ishaq!


Babu shakka awannan lokaci namu, zamu iya bugun gaba, muce munyi rashin gwarzon Namiji, haziqi, wanda abun duniya be dameshiba.


Wannan taliki, mutun ne wanda akoda yaushe burinshi shi ne yafarantawa yayan shahidai, ba wai a garin da yake zauneba a a!

Ako ina shahid ishaqa yake, yakanyi kokarin ganin yacika wannan alqawari na biyan haqqin shuhada'u.


Haqqin shuhada'u, wani haqqi ne da Aka salladawa kowane dan'uwa, ko yar'uwa.


Biyan wadannan kudade yana daya daga cikin alamun dake nuna cewa lallai kai cikakken mabiyin malan zakzaky (H) ne.


Babu shakka kowane wata an dorawa kowane dan'uwa biyan naira #100👌 akowane wata.

Zamu iya cewa biyan wadannan kudade yazama wajibi ga dukkannin yan'uwa.


Wadannan kudade da ake tattarawa na Hakkin shuhada'u!

Kudade ne da ake yiwa iyalan shahidai hidima.


Musamman abunda yashafi

1. Makarantun su

2. Suturar su/Tufafi

3. Kula da lafiyar su


Saboda girmamawa zuwa ga wadannan shahidai, shugabana kuma Jagorana, maulana shak Ibarahim Yakubu Al-zakzaki (H) ya kauwana wasu mutane daga cikin yan'uwa, ya basu Jagorancin *(Mu'assa-satushuhadau)*


Yakai me karatu, inaso kasan cewa shi wannan shahid ishaqa da muke magana.


Alamu sun tabbatar dacewa awajen wannan aiki na alheri, na biyan Wannan Haqqin shuhada'u. Wannan taliki Shahid ishaq baya wasa da biyan wannan Haqqi na shuhada'u.


Bayanan da muka tattara, sun tabbatar muna dacewa shahid ishaqa yakan taskace kudade aduk qarshen wata, domin biyan wadannan kudade na haqqin shuhada'u.


Wani lokacin ma yakan biyan na wata ukku, ko kuma wata shidda.


*Ta bakin mahaifinsa:*


Awata hira da nayi da mahaifin Shahid ishaq muhammad.

"Shahid ishaq Yakan nuna mun damuwarsa idan wata ya qare, kuma be biya haqqin shuhada'u ba.


Ya qara dacewa, wani lokacin yakan hada har da namu kuddin, dani da na mahaifiyar shi duka se yabayar."


"Yace, idan zakaje kaduba littafin da ake rubuta masu biyan Haqqin shuhadu, na tabbata bazakaga anbiyo shi na kowane wataba."


Bayanai sun tabbatar muna dacewa shahid ishaqa, mutun ne da rashin biyan Hakkin shuhada'u cikin lokaci, abun yakan damunsa sosai.

Bayanai sun tabbatar muna dacewa shahid ishaqa yataba saida wayar shi domin biyan Haqqin shuhada'u da ake biyarsa na kusan wata takwas (8)👌.


Babu shakka irin wadannan bayin Allah, nagar-tattun bayin Allah.


Abun koyi ne ga dukkan wani dan'uwa ko yar'uwa acikin wannan harka!


Amincin Allah yatabbata agareka ya Shahid ishaq!


Ranar haihuwarka

dakuma ranar da za a tasheka kana matsayin shahidi!!

Godiya ta tabbata ga ubangijin shahid ishaqa.


Godiya da yabo, ga ubangijin da yazzabeka amatsayin shahidi ya shahid ishaqa.


Godiya, da yabo da salati su tabbata ga manzon da aka aikowa shahid ishaqa !!


Daga qarshe muna fatan Allah yabarmu da soyayyarka ya shahid ishaqa!


Allah yabamu irin taku ya Shahid ishaq.!!


Godiya ta musamman zuwaga dukkannin ma'aikatan wannan shafi,na ma'asuma Nigeria news Update.


Wasallallahu ala Muhammad wa alihiddahirin!!👏🏽

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post