Rayuwa Ta Da Marhuma Khalisat M Kabir: "Tana Da Halin Girma Khaleesaty" Daga Jameel Ibraheem.. Fita Na Biyar (5)


 

Bayan mun yi waya, sai na shiga tunanin halin da take ciki, domin nasan ciwon wuya yana da wahala sosai. A wannan lokacin dai ya wuce, na cigaba da sha'anina ni na yi zatonma ta warke, ko irin nawa ne wanda na yi kwana kadan ya wuce, ashe nata na ajali ne.


A zo a yi muzaharar maulud na 12,watan Rabi'ul auwal. A lokacin ban shiga saminaka ba, bisa wani uzuri to sisters nawa sun shiga, sai nake baiwa Fauziya sako ta gaisheta in sun hadu, dayake Khaleesat ta santa sosai a dalilina. To bayan sun dawo, ban ji dai amsaba kuma ban tambayaba. Sai washe gari na ce bari na kira Khaleesat na ji wanna hali take ciki, a wannan lokacin na kirata to ta dauka tana magana sai na ji maganar bai fitowa kwata-kwata, ana yi amma ya rike a mako-garo. Anan sai na ji na canza, tausayi duk ya kamani. A lokacin sai na hakura na ce, na kirata daga baya ko da gobe ne, tun da ina ga kamar jikin ne ya tsananta.


A zo dai tun daga ranar kullum tunani na, ya jikinta ya yake,gashi kuma magana bata iyawa, A zo ranar Lahadi na(ana gobe zan koma school) na kirata anan na sameta har mu yi magana nake cewa: Ya jikin naki,kwanaki na kiraki na ji ban jinki maganar bata fita shiyasa ban kara kiraba, ki yi hakuri. Abun da ta ce:" Jiki babu dadi,yaki, karka damu ba komai ",nan sai na ji duk na canza yanayi,na ji hawaye ya zo min. Cikin rawar zuciya na ce, ki min afwa, wallahi na zo in zo in dubaki amma ban samu damaba gashi gobe zan koma da wuri. Ta ce karka damu, ba komai nagode, anan na ce 'Allah ya kara lafiya', ta ce:" Ilahi ajib lana ". A lokacin ban yanke wayarba sai na ji kamar tana son magana amma yaki, dayake dama maganar na bata wahala, ban dai katse kiranba anan sai credit ya kare.


Bayan wayanmu da ita, na tsaya sai tunani nake, sai na fara ji a zuciyata kamar rasuwa zata yi, nan dai na turo wannan tunanin. Haka dai na ta fama. Wallahi tun daga ranar ban kara samun cikakken kwanciyar hankaliba, kullum tunanin kenan ya jikinta. A zo gobe ta yi, na shirya ranar Monday na koma school a Kaduna. Ina cikin mota ba abun da nake tunani sai jikinta, zuciya tana saka min kamar rasuwa zata yo. Anan sai na sanya tawakkali, ni kadai cikin Zuciya nake cewa: In ma lokacinta ne yayi haka zata tafi ta barmu, nan na tuna irin halin da zamu shiga na kewa, sai kuma na ce: Ai cuta ba mutuwa ba ne, wasu sun yi fiye da haka sun kuma warke, nan na ce: Mutuwa ma ai ba sai kana jinyaba, in ta zo akwai hanyoyi da dama, accident ma mutum zai iya yi. Saboda haka Khaleesat zata samu lafiya in sha Allah. Haka nata fama, har cikin mota na tsargu, na fara tunanin kamar zamu yi accident, ko ya a kaucewa rami sai na ji zuciyata ta buga, haka dai cikin rashin kwanciyar hankali har na isa, mu sauka.


Bayan mun sauka, dayake gobe muna exams, na dauki littafi na dan duba, zuwa 1 na kwanta, asuba ta yi na tashi, ina tashi sai tunaninta ya zo min, nan a zuciyata ina da addu'a, "Allah ya baki lafiya Khaleesat",haka dai kullum da tunanin jikinta nake kwana in ta shi. Duk dai hankali bai kwantaba.


A zo, ina ji ranar Laraba ne, duk da nasan bata iya magana, saboda son jin ya jikinta yake hakan yasa na kira number nata, ina Kira kuwa a dauka amma ba ita ba ne, Sai mu gaisa nake cewa: Ina Khaleesat din, sai wanda ta dauka take cewa ai bata iya daukar waya, sai na ce Allah sarki, don Allah ki mata sannu, sai take cewa:" To,waye ne". Nan cikin rawar zuciya, saboda yanda na ji na bata iya daukar waya, duk na kideme, nan dai na ce ki ce kawai Jamilu ne, sai ta ce:" Ramin-Kura?",na ce eh, nan ta ce to zata ji. Na yanke wayar na zauna zuciyata sai bugawa take,na dade ina zaune.


Sai na ciro wayata, na bude data, na shiga Facebook lite, ina shiga naga an yi tag dina, ina dubawa naga ai post ne a yi a kan rashin lafiyar Khaleesat, ana fadin jiki yayi tsanani, bata iya ci bata iya sha. Nan hankaliba ya kara tashi, sai naga wani abokina dan Saminaka ya min magana, yana cewa "Amma kasan halin da Khaleesat ke ciki", na ce na sani, har yake fadi min cewa:" Kwananta kusan 12 ba ci ba sha ",nan na ji hawaye. Can bayan haka, da kwana daya sai mu yi chat da wata kawarta, itama labarin kenan, can wani abokina ya kiran, shima duk labarin kenan jikinta ya tsananta.


Na zo,ranar alhamis na kwanta, sai kawai na yi mafarkin yanayin jikinta. Ciki naga lallai tana shan wahala, duk ta rame, kamar ba itaba. Da na tashi na yita fadin Allah ka bata lafiya.


Mu zo mu samu Interval a exams na 1week, anan na ce, zan kuma gida kawai duk da ban wuce kwana hudu da dawowaba, na koma dai gida a ranar Jumma'a, mu isa da kusan magriba. Washe gari asabar haka, sai mu na tsara akan zan je na dubata gobe Lahadi, to a lokacin ma ni na yi zaton suna gida ne, aban labari ai ba su gida, suna asibiti. Duk dai na shirya kan goben zan je in dubata.


A ranar asabar da yamma zuwa dare, labari ya kara zuwa kan cewa jikin ya tashi, sai aman jiniba take, harma in ta fara sai a tare a bokati, nan naji hankaliba ya tashi sosai fiye da da, na ji ciwon kai ya zo min, na sha magani na shiga daki tun kafin isha'i, na yi sallah na a daki, na dauko wata addu'an biyan mukata, na imam Ali assajad, na karanta,dayake dama tun daga talata kullum ina karanta mata kan Allah ya bata lafiya. Na zauna can, na kwanta bacci ya dauken.


Washe gari, Lahadi karfe kusan 11, sai na Kira number na Khaleesat (nasan ba dole ba ne in sameta, amma zan iya samun wata ta daga kiran, sai na sa a mata sannu) a lokacin ina Kira sai a daga, ayi shuru ba magana, na yanke na kara kira, nanma a daga shuru ba magana, nima dai ban yiba. sai na fara tunanin ko Khaleesat din ce ta daga, ta kasa yin magana (domin wata ba zata dagaba taki magana, a kara ta daga taki magana, dole in da wata ce zata yi magana) nan dai na sake kira a na uku, sai a kara dagawa sai naji kamar ana yunkurin magana, lokacin sai na bari kan ita ce kawai, sai na fara magana ina cewa: Aslm,ba amsaba, nan na ce: Itn wayar bata hannunki ne, don Allah wacce take hannunta ta yi mata sannu, Allah ya bata lafiya. Gefe can sai na ji magana, ana fadin waye ne? Ana mata(ban ji da kyauba,kamar dai ana mata addu'a), sai na katse wayar dai. na yi shuru na shiga daki, na turo na zauna kan kujera ina ta addu'a a cikin raina, Allah ya bata lafiya. Nan sai na yi text message ta number na Khaleesat din, nake cewa "Assalam,fatan jiki yayi sauki.Allah ya kusanto da waraka alfarman mafi daraja Muhammad s.a.w.w.Allah ya sa kaffara ce.Sannu da jiki! Me yuwuwa wayar ba a hannunki take ba,dazu na kira dama ko wata ta dauka na ce a miki sannu da jiki ne,amma an dauka ba a magana. yanzun ma in wayar bata kusa dake, wacce take kusa da ita afwan ta miki sannu da jiki Allah ya sauwaka". Na aji wayar.


Na kara daukar wayar, sai na hau Facebook, ina hawa sai naga post na yayanta Mallam Saifullahi, kan cewa "Za a shiga da ita dakin surgical room. Nan dai na sauka, shima sallar Azahar a daki na yi, bayan idar na kamo wanan addu'a da na saba karantawa, nan shima na karanta. Bayan haka sai na sanyawa zuciyana kan in sha Allah za a fito lafiya.


Na zauna na yi ta tunani haka dai, har nake cewa Allah sarki, na dawo daga Kaduna sun kuma tafi can, zan koma Jumma'a in na koma na je na gaisheta, tun da a Kaduna ne asibitin.


Zan ci gaba ...


Allah ya sanya sayyada Zahra a.s ta karbi bakoncinki Abokiyar Mutumci "Khaleesaty", don darajar annabin Rahma, Muhammad s.a.w.w.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post