ADDINI BA YA YIWUWA SAI DA ILIMI: Ku Tambayi Ma'abota Sani Idan Ku Baku Sani Ba !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Za ka samu da yawa an qirqiri wani abu mai kyau ko da kyakkyawar manufa wanda zai iya kawo cigaba cikin al'umma, sai dai idan akayi rashin sa'a jahilai suka yi yawa a ciki ko kuma sune jagorori, to, sai kaga ba a cimma abinda ake son cimma masa ba. 


Ita kuwa harkar da'awa ta muslimci ita tafi komai muhimmanci kuma take da qalu-bale wanda kan iya dabaibaiceta matuqar anyi sake cikinta. 


Za ka sami jagororin da'awa da fikira da kuma aikata abinda ya dace wanda zai iya jawo hankalin al'umma su fahince su tare da amsa musu. Amma idan aka ce an sami jahilai masu yawa cikin tafiyar sai ya zamana cewa suna fassara wannan da'awa da wani abu na dabam wanda ba koyarwar ta bane. 


Jahilci ba qaramin ciwo bane, domin yakan cutar da mai shi da kuma cutar da wasu sakamakon aikata aiki cikin Jahilci. 


Matasa sune ginshinqi na kawo cigaba da fata na gari cikin kowacce tafiya, amma idan aka ce jahilci ya dabaibaice su sukan zama annoba cikin al'umma ko kuma cikin kowacce tafiya. Dalili kuwa shine, sukan iya hanawa ruwa gudu ta wani bangaren sakamakon ayyukansu na jahilci, ko kuma su riqa haifar da matsaloli masu wuyar magancewa. 


Abu mafi muhimmanci kuma wajibi gare su shine su tashi su nemi ilimi ta hanyar karatu da kuma yin tambaya kan dukkan wani abinda basu san hukuncinsa ba .


Allah (T) na fada cikin Alqur'ani mai tsarki cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" فَسْئَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ‏."


" KU TAMBAYI MA'ABOTA SANI IDAN KUN KASANCE BA KU SANI BA ."


Wannan umarni kuwa yana kan kowa ne, manya da yara ko maza da mata, domin cikin kowanne bangare ana samun jahilai masu aiki cikin jahilci. Aikinsu na jahilci kuwa ba zai zama alkhairi cikin wannan da'awa ta Sayyid Zakzaky (T) ba. 


Duk wanda zai yi karatu ko ya riqa tambayan agun wanda ya sani, to, zai kyautata rayuwarsa ya zama abin koyi kuma mai amfanar da al'umma. 


Yazo cikin hadisi kamar haka; 


1- ل، الخصال ابْنُ الْمُغِيرَةِ بِإِسْنَادِهِ عَنِ السَّكُونِيِّ عَنْ جَعْفَرٍ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: الْعِلْمُ خَزَائِنُ وَ الْمَفَاتِيحُ السُّؤَالُ فَاسْأَلُوا يَرْحَمُكُمُ اللَّهُ فَإِنَّهُ يُؤْجَرُ فِي الْعِلْمِ أَرْبَعَةٌ السَّائِلُ وَ الْمُتَكَلِّمُ‏[1] وَ الْمُسْتَمِعُ وَ الْمُحِبُّ لَهُمْ.


Daga Ibn Mugeerata da isnadinsa daga Sakuniyyi, daga Ja'afar daga babansa (A. S) yace:


" SHI ILIMI (wata) TASKA CE, KUMA MABUDINTA SHINE TAMBAYA, KUYI TAMBAYA (sai) ALLAH YAYI MUKU RAHMA, DOMIN (jinsi) HUDU (4) SUNA SAMIN LADA. 


(1)- MAI YIN TAMBAYA (don neman sanin abinda bai san shi ba), 


(2)- DA MAI YIN MAGANA (malamin dake karantarwa ), 


(3)- DA MAI SAURARE (yayin da ake karatu ko bada amsar tambaya), 


(4)- DA MAI SO (ya ji ana karatu). 


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏1، ص: 197


Sai dai wani abin mamaki shine, sai kaga mutun mai qoqari wajen bayar da lokacinsa akan harkar addini har ma yana bada jininsa don bawa addini kariya, amma idan aka zo bangaren karatu sai ya baka kunya. Irin wadannan suna daga cikin wadanda Annabi (S. A. W. W) ya ambace su a matsayin annoba cikin muslimci. Kamar yadda ya ce, " AL-MUJTAHIDUN JAAHILUN ." (Jahili mai qoqari). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


         (08126385470)


17th November, 2020/ 1st Rabi'us-Sani, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post