Me Yasa Da Yawa Daga Cikin 'Yan Mata Suke Rabuwa Da Samarinsu, Bayan Sun Ci Gaba Da Karatu A Makarantar Gaba Da Sakandari?.. Fita Na Biyar (5)


Bismihi ta'ala


Nayi magana da dan dama akan wannan matsala din, kuma insha Allah wannan ne rubutuna na karshe akai, ina godiya da lokutanku da kuka bani.


Ammm a iya dan tunanina da kuma hasashena, wannan matsalar kowa yanada hannu aciki, bawai laifin mata kadai bane, ko kuma laifin maza maza, Aa kowa nada sa hannu aciki hada iyaye ma.


Kuma maganin wannan matsalar shine, mu komawa Allah gaba daya, saboda duka damuwar tana faruwa ne idan an kaucewa tsarin da Allah ya umarta da mubi, kenan idan har muka koma son junanmu tsakani da Allah, kuma saboda Allah ba don wani abun duniya ba, to lallai zamu daina samun irin wannan matsalar gaba daya.


Saboda dama dayawan matsalar da muke samu a rayuwarmu banda wacce duk rintsi bama iya kauce mata, ma'ana kaddarar da Allah ya rubuta Mana, to dayawa mune muke haifama kanmu ita da kanmu, ta hanyar bijirewa dokokin Allah, Kuma da munga ba daidai ba sai mu ce Allah ne, bayan mu muka haifama kanmu ita da kanmu.


Saboda haka a karshe nake rokonmu da don Allah, mu daina biyewa abin duniya muna cutar da abokanan rayuwarmu, shifa arziki da talauci duka na Allah ne, idan ya nufa zaka samu to ba wanda ya isa ya hanaka shi, haka idan bai nufa ba to duk wayonka bazaka iya samama kanka shi ba.


Mu dogara dashi tunda shike badawa, Allah ya zaba ma kowa abinda yake alkhaeri a gareshi, ya hadamu da masu sonmu tsakani da Allah, ya hanamu cutar dasu saboda abin duniya.


Nagode sosai da lokacin da kuka bani, Allah ya bar zuminci.


✍️_ zarah A zamsarf

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post