Kogin So, Fadawa Ba Wahala, Fitowa Lafiya Sai Mai Sa'a. Kashi Na Takwas (8)


 Rbtw: J. I. R


Su zauna da kakanta Hadiza su yi ta hira, karshe dai ta tashi ta samu Asma'u wacce take a gidan, akan su fita yawo don ganin gari, tare da gaishe-gaishe. Da su fita Asma'u ta rakata gidaje da dama ta yi gaisuwa. Har magriba ta yi su dawo gida.


To rayuwarta dai a kauyen nan, ya ci gaba tana yawonta, tare da Asma'u, ana nan-ana nan wata rana sai suka tafi ta wurin aikin hanya(titi). Don ganin wurin.


Zuwansu ke da wuya, sai mai kwangilar hanyar nan ya hango Zainab, har ya ji da yana sonta, shi dai Alhaji Hudu mutum ne mai kudi sosai. Wanda yana zaune ne a cikin garin Kano.


A lokacin Alhaji Hudu ya je ya samu su Zainab kan bayyana manufarsa, amma kash Zainab bata sauraresaba. Ta nuna bacin rai sosai.


Su Zainab sun koma gida, Zainab ranta ya baci sosai. Domin kuwa tana da wanda take so, kuma wani ya zo yana neman shiga rayuwarsu. Abun dai bai mata dadiba.


Washe gari, kwatsam! Sai ga Alhaji Hudu kofar gidan su kakan Zainab, ya zo gun Zainab don bayyana manufarsa kanta. Ya zo cikin shiga na girma, tare da babban motarsa, da ya zo yayi parking a kofar gidan, ya sanya wani yayi sallama da Zainab. Yaron da ya aika ya Kira Zainab ya je, "Salamu alaikum, ana sallama da Zainab", budan bakin ta caraf ta yi ta ce, "Waye ne? Ka ce bazan zoba", a take sai kakanta Hadiza ta ce, "Haba Zainab ki fita mana kiga ko waye, in ya so Kya dawo", Zainab ta ce, kaka ni bazan fitaba. Kakanta Hadiza ta rarrasheta a kan ta fita ko da tana zuwa ta dawo ne. Yaron nan ya tafi ya ce, "Gata-nan zuwa" a take Alhaji Hudu ya dauki Dubu goma ya baiwa dan aike, ya ce, "Na gode yaro". Zainab ta fita da kyar.


Tana fita ta ci karo da babban mota, cikin lokaci taga an fito cikin wanan motan, ganin ke da wuya sai taga wanan Alhaji ne, da ya tsare su a shekaran jiya wurin wanna aikin hanya.


Alhaji Hudu nan ya fara zub da zance, domin bayyanar da manufarsa ta hanyar da yana ganin za a iya fahimtarsa. Yana cewa, "Mallama Zainabki yi hakuri, duk da cewa na bincika naga ke bakuwa ce a wannan kauyen, kamar yadda nima din bako ne, kuma na bi hanyar da ya dace don jin ke wacece, kuma an min bayani sosai. Na aminta dake, ki aminta dani. Ni dai suna na Alhaji Hudu, ina garin Kano, kuma ni ke kula da wanan aikin na hanya da ake yi a wanna kauyen, Kuma ni sonki nake da aure. Na same ki ne don in sanar dake don jin ra'ayinki", Zainab ta ce, "Zainab budan bakinta ta ce, gaskiya ka yi hakuri ina da wanda zan aura", Alhaji Hudu ya ce, "In dai ba an sa auren ba ne, to ni ba damuwa a guna". Haka nan dai su ta fama. Su rabu ba tare da Zainab ta fahimcesaba. Da zai tafi ya dau Kudi masu yawa ya bata, taqi amsa, ya ce, "Aa ki amsa, raboki ne, karki bar rabonki", ya takura dai sai da ta amsa. Ya shiga motarsa ya tafi, ita kuma ta koma gida.


Tana zuwa, sai kakanta ta hangota da kudi, nan cikin hanzari ta zo ta sameta, "Kai Zainabu ke arziki ne ashe ki kiranki da kiqi fita", nan ma Asma'u ta zo, sai Zainab ta nema su kebe da Asma'u don shawara, a lokacin da su kebe sai Zainab ta baiwa Asma'u labarin yadda suka yi da Alhaji Hudu, kuma ta bata labarin cewa ita tana da saurayinta, kuma yana sonta. Anan sai Asma'u take cewa, "Shi din waye? Zainab, kin san fa shi rayuwar nan inda za a huta ake zuwa, Zainab wallahi in ki so wanna mun huta muma bakeba". Zainab ta ce, "Haba Asma'u, Ahmad ne, yana sona, shi din dai ba kowa ba ne kuma ba dan kowaba", Asma'u ta ce, "To yanzu dai ni dai na baki shawara wannan shi ne alkahiri gareki, domin zaki huta.


Haka dai Asma'u ta yi ta cusawa Zainab ra'ayin Alhaji Hudu, shi ko sai sake mata kudi yake, har ya zo ya gana da kakan Zainab, itama ya aje mata kudi da yawa. Ya ja hankalinsu da kudi sosai.


A zo Zainab ta fara son Alhaji Hudu, bata dai bayyanarba, to ana haka.


Wata rana sai Ahmad ya Kira Zainab, ya sameta yake cewa, "Haba Sweetheart, ki tafi kin barni, ko ki nemen, kin san garin da kike ba a nemanku a sameku sai an ci sa'a, gaskiya hakan ya dada min radadin kewarki", nan sai Zainab ta ce, "Ka yi hakuri My, na yi laifi, fatan kana lafiya, ka kwantar da hankalinka zai dawo gareka lafiya, kuma ina kara fadima kai ne jarumina", Ahmad ya ce, "Na gode, sai anjima, ki kula min da kanki, ki gaishe da su kaka".



Mu hadu a kashi na gaba, don jin ya Zainab zata yi? ko za ta kara adana soyayyar Ahmad ne.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post