Da yawa da ga cikin Hausawa musulmi ƴan Arewa, musamman matasa maza da mata da su kayi fice ta hanyar Film waƙa da makamantan su, su kan su ba su san sun yi sunan da za a iya amfani da su ta hanyar cutatawa Addinin su ba.



Zaharaddeen Mziag 04/11/2020


Idan muka tsaya tsaf muka lura dakyau akan abinda ke faruwa akan musamman mawaƙan hausa musulmi ƴan Arewa zamu fahimci cewa ana amfani dasu ne, ana mana HARBUN NA'IMA (Soft War) yaƙin ruwan sanyi ne.


Ƙila dayawa (mawaƙan suce a'a) saboda zasuga cewa kamar du abinda suke aikatawa sunayi ne don kankin kansu, babu wani daga cikin maƙiya musulinci da ya taɓa gewayo wa a ɓoye ko a baiyane yabasu wata awalaja akan cewa ga abinda akeso suyi na ɓata tarbiyyar musulmi ƴan uwansu.


Idan har ka sake kayi wan'nan tunanin lallai kafaɗo ƙasa warwas, saboda kai kanka kana iya zama kayan aikin yahudu batare da kasani ba, wan'nan kuwa shi'akecewa yaƙin ruwan sanyi.


Yakamata mudawo hayyacin mu, mu Hausa fulani ne,kuma mu musulmi ne, munada Al'ada muna da Addini, tunda dukkan mu munce;


 La'ilaha Illallahu Muhammadu Rasulullahi! 


Kenan munada Nizami, munada tsarin da muke a ƙarƙashin sa, don haka dole ne garemu mubi tsarin da yake ƙarƙashi wan'nan kalmar mai girma, duk abinda yazo na Halas a ƙarƙashin kalmar muyi shi komin wahalar sa, haka kuma duk abinda yazo na Haram a ƙarƙashin kalmar muyi ƙoƙarin barin sa komin Burgewar sa.


Idan muka tsaya akan wan'nan tsarin bamu kauce ba wallahi ko sheɗan babu yanda zaya'iya damu. To amma munbar tsarin mun ruɗu da ɗabi'un yahudu suncimu da yaƙi, wasun mu ma kwatakwata suna barin Addinin su, sukoma suna yaƙi da shi.


Wasu kuma suna cikin musuluncin amma zuciyar tana Amerika cikin turawan yamma, 


Rahama Sadau dai anriga ya ankoreta daga cikin masana'antar KANYWOOD, saura dami? wasu daga cikin mu musulmi ƴan komi Bidi'a sufitar da ita daga musulinci, inyaso shike nan munrasata sukuma maƙiya sun samu, sai su karɓeta hannu biyu, ta ɗora daga inda ta tsaya kuma tayi mukalla muji haushi, babu yanda zamuyi da ita, saboda dokar da ba ta Allah ba tabata ƴanci.


Ni inaga Nasiha da jawota ajiki da kwatantamata shine matakin da ya dace ba caccaɓamata maganganu a Social Media ba, wan'nan maganar da ƴan Film ƴan'uwanta nake, saboda sunada hanyar da zasubi suyi mata nasiha tsakanin su da ita ba wai suzo social media suna huce fushin su ba.

 

Ba ina kareta bane, nasan ita ƙila da ire irenta basu gane cewa tayi sunan da za'a iya yaƙar Addinin ta da ita ba, amma dai wan'nan darasi ne. Saboda shi, hannun maƙiyi tsawo gareshi tako ina kai caffa yakai, mutaka a sannu.


Wan'nan Hotunan wasu mawaƙa da ƴan film ne da suke shigar da ta saɓawa Al'ada dakuma Addini, kuma kowanne daga cikin su maƙiya na iya amfani dashi domin cinma buƙatun su ko ya sani ko bai sani ba. Mafita kawai mudawo ma tsarin Allah kada son duniya ya jefa mu a santsi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post