Batancin Kasar Faransa Ga Manzon Allah Laifin Musulmai ne. – Cewar Sheikh Yaqub Yahaya Katsina.


@Isma'il Abubakar Idris Katsina.


Manzon Allah ramzi ne, abin koyi ne ga dukkan halitta kowa da kowa, abin da Kasar Faransa tayi laifine babba amma mafi munin laifin yana wajen Musulman Duniya musamman bangaren Sunni.


Tabbas abinda Kasar faransa tayi laifin na musulmai ne, doqmin a cikin litttafan muslunci suna fadi siffofin Allah da na Manzon sa Annabi (S.a.w.w) idan da za'a dauko mai zane ana karanta littattafai irin nasu Buhari ko Muslum da sauran su tabbaswani mai zane zai iya zanawa kamar yadda Faransa sukayi, ba abin mamaki bane dan ance wani ya zana Manzon Allah.


Idan kaduba cikin Littafin Bukhari da Muslum suna siffanta Allah da Manzon sa cikin mummunar siffa ko suce Mutum ne kamar kowa ko yana fitsarin tsaye da maka mantansu, Babu yadda za'a samu wani Littafi koda guda 1 ne cikin Littattafan shi'a wanda zai siffanta Annabi kwatan kwancin irin na Bukhari ko Muslum.


Shugaban Kasar Faransa na cewa "Ina mamakin yadda Musulman Duniya keyiman zanga-zanga dan wani ya zana Annabi, yakamata Musulmai su fara yiwa Sahabbai zanga-zanga su fara yiwa kansu Zanga-zanga sabida duk abinda kukaga an zana akwai shi cikin littattafan Buhari".


Shugaban Kasar Faransa ya bada sunan litta da Lambobin Hadisin da aka fadi surorin Annabi. Duk maiso ya nemi firar da akayi da shugaban Faransa akan batancin da sukayiwa Annabi yananan an fassaraci cikin yaren Larabci.


Sheik Yaqub Yahaya a wajen taron Maulud na 17 a Markaz Katsina a yau Talata 17/03/1442 wanda yayi dai dai da 03/11/2020. Da misalin karfe 06:00Pm.
 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post