YARDADDU BIYU ABABAN YARDEWA: Al-Muratada, Yardadden Allah Daga Sama


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Babu shakka duk wanda yayi riqo da wanda Allah ya yarje masa ya sami gwaggwaban lada a duniya tare da samun aminci a lahirarsa. 


Imam Ali (A. S) bai sami wannan laqabi (AL-MURTADAH) bisa hadari ba, a'a, ya same shi ne bisa qudura ta Allah don ya nuna wani matsayi nasu (A. S) cikin al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W). 


Annabi (S. A. W. W) ne ya kiraye shi da wannan suna bisa hujjarsa kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


وَ فِي خَبَرٍ أَنَّ النَّبِيَّ ص سَمَّاهُ الْمُرْتَضَى لِأَنَّ جَبْرَئِيلَ ع هَبَطَ إِلَيْهِ فَقَالَ يَا مُحَمَّدُ إِنَّ اللَّهَ تَعَالَى قَدِ ارْتَضَى عَلِيّاً لِفَاطِمَةَ ع وَ ارْتَضَى فَاطِمَةَ ع لِعَلِيٍّ ع.


Ya zo cikin labarai (masu tushe) cewa, lalle Annabi (S. A. W. W) ya ambaci ne da MURTADHAH saboda mala'ika Jibrilu (A. S) ne ya sauko gare shi yace; 


" YAA MUHAMMAD, LALLE ALLAH (T) YA YARJEWA ALIYU FADIMATU (S. A), KUMA YA YARJEWA FADIMATU (S. A) ALIYU (A. S) (don su zama abokan zama a Matsayin ma'aurata) ."


__________________________

(1) ساط الحرب: باشرها. و في المصدر: لانه أعلى من ساجله. و معنى ساجله باراه و فاخره.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏35، ص: 60


Ibn Abbas (R. A) kuma yace, 



وَ قَالَ ابْنُ عَبَّاسٍ‏ كَانَ عليا [عَلِيٌ‏] ع يَتَّبِعُ فِي جَمِيعِ أَمْرِهِ مَرْضَاةَ اللَّهِ وَ رَسُولِهِ فَلِذَلِكَ سُمِّيَ الْمُرْتَضَى.


" Aliyu ya kasance yana bibiyar komai nasa don neman yardar Allah da Manzonsa ne , saboda haka aka ambace shi da Murtadhah ."


Wannan suna ya dace da shi, domin shi kadai ne cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) ya aikata dukkan umarni Allah ba tare da an bi shi bashin wani abu ba. Za ku tabbatar da haka in kuka duba Tafsirin ayar nan da ke cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


"YAA KU WADANDA SU KAYI IMANI ! IDAN ZA KU GANA DA ANNABI KU GABATAR DA SADAQA GABANIN GANAWAR TA KU ....."


Babu wanda yayi aiki da wannan ayar har aka soke ta. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


 08137925034-08126385470


26th Sep, 2020/ 9th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post