Sharrin Munafikan Yanzu Yafi Na Zamanin Annabi (s.a.w.w) !!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Ba zai rasa nasaba da zamani ba tare da lalacewar al'ummar dake cikin zamanin. Kamar dai yadda hausawa ke cewa wai " IN DAMBU YAYI YAWA BA YA JIN MAI ."


Ko da shike wannan Karin Magama ta malam bahaushe ba za ta zama hujja abin gamsarwa ba, domin rashin jin man nasa rashin wadata ne, amma ku tambayi azzalumai masu yin rub-da-ciki kan dukiyar al'umma kaji ko wannan tsadar abincin na damunsu ko iyalansu na cin shinkafa a bushe ba mai sai yaji ? 


Gaskiyar magana dai ita ce qeqashewar zukatan Al'umma ne da rashin rabon lahira yayi sanadin bayyanar da munafurcin nasu a fili fiye dana zamanin Annabi (S. A. W. W), domin na zamanin nasa (S. A. W. W) sai an saukar da aya a kansu ake gane su qarara, amma a wannan zamani ba sa buya don duniyar ce kadai a gabansu. 


Tun daga barin Annabi duniya munafukai suka fara bayyanar da munafurcinsu a zahiri kamar yadda Huzaifatul-Yamani ya fada kuma aka kawo shi cikin Bukhari kamar haka; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


" LALLE MUNAFUKAN YANZU SHARRINSU YA FI NA ZAMANIN ANNABI, A WANCAN LOKACIN SUNA BOYEWA, AMMA A YANZU BAYYANAR DA SHI SUKE YI ."


(Bukhari, hadisi na 7113)


Wannan maganar tasa yayi ta ne (immediately) bayan wafatin Annabi (S. A. W. W), to, ya kuke ganin sharrin munafukai na wannan zamanin da muke ciki ?


YAA ALLAH KA SHIGA TSAKANINMU DA SU. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


          (08137925034)


16th Sep, 2020/ 28th Muharram, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post