Sayyidah Maryam Da Fatimatu (S.A) Kadai Ake Kira Da Batula !!!@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MA'ANAR SUNAN BATULA 


Da yawa za muji ana sanyawa yara mata suna Batula kuma yaran suna fahari da wannan suna domin sun ji ana cewa sunan Sayyidah Fatimah (S. A) , amma basu ma'anar sunan ba, alhali duk wani sunanta na da ma'anarsa. 


Ga riwaya daga Imam Ali (A. S) inda yake cewa; 


مع، معاني الأخبار ع، علل الشرائع بِإِسْنَادِ الْعَلَوِيِّ عَنْ عَلِيٍّ ع‏


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 أَنَّ النَّبِيَّ ص سُئِلَ مَا الْبَتُولُ فَإِنَّا سَمِعْنَاكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ تَقُولُ إِنَّ مَرْيَمَ بَتُولٌ وَ فَاطِمَةَ بَتُولٌ فَقَالَ ع الْبَتُولُ الَّتِي لَمْ تَرَ حُمْرَةً قَطُّ أَيْ لَمْ تَحِضْ فَإِنَّ الْحَيْضَ مَكْرُوهٌ فِي بَنَاتِ الْأَنْبِيَاءِ.


An tambayi Manzon Allah (S. A. W. W) cewa me ake nufi da Batula domin mun ji ka yaa Ma'aikin Allah kana cewa Maryama Batula, Fadimatu Batula . Sai yace; " AI BATULA ITA CE WACCE BATA TABA GANIN JAJA-JAJA BA (ruwa mai kalar jini na fitowa daga farjinta ba), MA'ANA AI BATA TABA YIN HAIDHA BA, DOMIN HAIDHA ABIN QI NE CIKIN 'YA'YAN ANNABAWA ."


Dangane da ma'anar sunan Fatimah kuwa an samo riwaya daga Imam Ja'afarus-Saadiq Bn Muhammad Baqir (A. S) yace, 


- قب، المناقب لابن شهرآشوب ابْنُ بَابَوَيْهِ فِي كِتَابِ مَوْلِدِ فَاطِمَةَ وَ الْخَرْكُوشِيُّ فِي شَرَفِ النَّبِيِّ ص وَ ابْنُ بَطَّةَ فِي الْإِبَانَةِ عَنِ الْكَلْبِيِّ عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ ع قَالَ:


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لِعَلِيٍّ هَلْ تَدْرِي لِمَ سُمِّيَتْ فَاطِمَةَ قَالَ عَلِيٌّ لِمَ سُمِّيَتْ فَاطِمَةَ يَا رَسُولَ اللَّهِ قَالَ لِأَنَّهَا فُطِمَتْ هِيَ وَ شِيعَتُهَا مِنَ النَّارِ.Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Imam Ali (A. S) ,


" SHIN, KA SAN DALILIN DA YASA AKA AMBACETA DA FADIMA ?


Ali yace, don me aka ambace ta da Fadima yaa Ma'aikin Allah ? Yace; 


" DOMIN AN FANSHETA NE DA 'YAN SHI'ARTA DAGA WUTA ."


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 16Daga wakilanmu na Bauchi. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        08137925034


27th Sep, 2020/ 10th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post