Sayyida Sakinah (AS) A Tarihin Musulunci .....

 


 _- Abdullahi Isah Wasagu_ 


Muna taya al'ummar Musulmi musamman mabiya Mazhabar Ahlul Bayti (AS) jimamin Shahadar Sayyida Sakinah (SA). 


Sayyida Sakina wadda harwayau ake kira Sayyidah Rukayyah (AS), 'yar Imam Hussaini (AS) ce, waccen ta kasance tana daya daga cikin Ahlul Baytin Manzon Allah wadda ta ga yakin Karbala.


Sayyidah Sakinah ta yi Shahadah ne a irin wadan nan ranaku wato, 13 ga watan Safar.


Ta yi Shahadah ne a gaban Imami na 5, wato Imam Zainul Abideen wanda shi ma dan Imam Hussaini ne, wanda shi kadai ya yi saura a cikin Sahabban Imam Hussaini su 72 a mafi yawan ruwa.


Kammar yadda yazo daga Malaman Tarihi, Sayyida Sakinah ta samu wannan lakabi ne na suna, "SAKINAH" a irin lokutan da take yawan kwanciya a jikin Imam Hussaini (AS) tsawon lokuta. Wanda idan dare ya yi; Imam yakan ce, "Lokaci ya yi da ya kamata ki samu "SAKINAH" ya Rukayya. Sai Imam Hussaini ya kama hannunta ya kaita wajen Ummanta Sayyida Zainab (AS).


Sayyida Sakina ta kasance bata son rabuwa da Abbanta Imam Hussaini (AS). Ya zo a cikin tarihi cewa, idan dare ya yi, kafin ta kwanta barci, idan ta zo ta jigina da jikin mahaifinta, Imam Hussaini (AS) yakan karanto mata tarihi da kyawawan dabi'un Kakanta Manzon Allah (SAWW). Haka nan, ya kan karanto mata tarihi na irin yakoka da Kakanta Imam Ali (AS) ya yi a zamaninsa.


Sayyida Sakinah ta ga bala'o'i daban-daban a rayuwarta tamkar Imam Hussaini (AS). Rayuwa ya zamo gwarwashin wuta tun daga ranar 8 ga watan Muharram, ranar da ruwansha ya yanke a tantin su Imam Hussaini (AS).


Sayyidah Sakinah ta kasance tana kuka na irin ukubar da suke fiskanta da yayanta Imam Zainul Abideen (AS). Tana daga cikin mata iyalan Imam Hussaini wadanda aka ja su a kasa cikin turbaya; babu takalma; ga kunar zafin rana tun daga filin Karbala har fadar Yazidu dan Mu'awiya bayan sun kashe Imam Hussaini da dukkan Sahabbansa a filin Karbala.


Assalamu alaiki ya Sayyida Sakinah !

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post