Ko Kunsa Yadda Ake Shari'ar Su Mlm Zakzaky (h) Tundaga 2018 har Zuwa Yau ???



 Zaman kotu (a takaice) na Case din su Malam Zakzaky (H) daga 2018 zuwa yau


Daga Abdulmumin Giwa


Case din nan da ake karar su Malam, tun farko an shigar da shi ne a matsayin gwamnati na karar Malam da Malama da Mal Yakubu Yahaya da Mal Sanusi Abdukkadir.


Ba a samu mikawa Mal Yakubu da Mal Sanusi sammacin kotu ba inda har aka dage zama zai kai kashi uku ko fiye. 


Sai kuma daga baya aka dawo kotu aka raba case inda gwamnatin Kaduna ta sake shigar da karan akan Malam da Malama kawai. A nan an cire Mal Yakubu da Mal Sanusi daga case din, su za a yi nasu daban. 


Sai kuma aka kawo maganan zuwan su Malam India domin neman magani. Duk a wannan lokaci ba a fara case din ba saboda an ce sai da lafiya za a iya case.


Aka dawo daga India kuma lokacin ne alkalin ya tafi aikin Elections Tribunal wato kotun shari'o'in zabe da aka yi. Bayan ya dawo daga tribunal ne kuma aka kawo maganan barin likitocin Malam su rika ganin Malam a Kurkuku inda kotu ta ba da dama a bari a rika ganin sa.


Daga nan kuma an zo an shiga lokacin COVID-19. Wanda ba a sake zama ba sai da aka gama lockdown.


An dawo an sa case kuma aka samu wani case din da aka dage saboda ya fado a ranar hutu. A duk wannan lokaci da aka raba case ba a karanta wa su Malam abin da ake karar su akai ba sai yau, inda kuma suka ce "Rubbish and nonsense" ne  wanda yake nuna bai amsa zargin da ake yi masa ba.


Alkali kuma ya ce masu kara su kawo shaidun su tunda wadanda ake kara ba su amsa zargin da ake musu ba, a ranakun 18 da 19 na November don yana so a gaggauta kammala case din da aka fara tun 2018.


Wannan dai a takaice, abubuwan da suka faru a kotu kenan tun da aka shigar da kara.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post