Ma'asumah: Da Ba Don Ali Ba Da Bata Da Abokin Hadi Har Abada!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


SAYYIDAH FATIMA (S. A) NA DA SUNAYE 9 A WAJEN ALLAH 


Matsayin shugabar matan talikai baki daya Sayyidah Fatima (S. A) ya wuce tunanin duk wani mai tunani. Zababbiya ce wajen Allah, kuma tsarkakekkiya abar tsakakewa, shi yasa ba ta da abokin hadi in ba zababbe tsarkakekke irinta ba. 


Tarihi ya tabbatar da cewa mutane da dama kuma cikinsu har da masu kudi sun nemi aurenta wajen mahaifinta (S. A. W. W), amma bai basu ba saboda shima ba shi da iko da ita in ba Allah ba. 


Riwaya zuwa kan Abu Abdullahi (A. S) yana cewa; 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


1- لي، الأمالي للصدوق ع، علل الشرائع ل، الخصال ابْنُ الْمُتَوَكِّلِ عَنِ السَّعْدَآبَادِيِّ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ عَبْدِ الْعَظِيمِ الْحَسَنِيِّ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ يُونُسَ عَنْ يُونُسَ بْنِ ظَبْيَانَ قَالَ قَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع‏


-------------------------------------------


 " لِفَاطِمَةَ ع تِسْعَةُ أَسْمَاءَ عِنْدَ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ فَاطِمَةُ وَ الصِّدِّيقَةُ وَ الْمُبَارَكَةُ وَ الطَّاهِرَةُ وَ الزَّكِيَّةُ وَ الرَّاضِيَةُ وَ الْمَرْضِيَّةُ وَ الْمُحَدَّثَةُ وَ الزَّهْرَاءُ ثُمَّ قَالَ ع أَ تَدْرِي أَيُّ شَيْ‏ءٍ تَفْسِيرُ فَاطِمَةَ قُلْتُ أَخْبِرْنِي يَا سَيِّدِي قَالَ فُطِمَتْ مِنَ الشَّرِّ قَالَ ثُمَّ قَالَ لَوْ لَا أَنَّ أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ ع تَزَوَّجَهَا لَمَا كَانَ لَهَا كُفْوٌ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ عَلَى وَجْهِ الْأَرْضِ آدَمُ فَمَنْ دُونَهُ."


                FASSARA 

              ------------------


" FADIMATU NA DA SUNAYE TARA (9) WAJEN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA , 


-FADIMATU da 


-SIDDIQAH da 


-MUBARAKA da 


-'DAHIRATU da 


-ZAKIYYAH da 


-RADHIYYAH da 


-MARDHIYYAH da 


-MUHADDITHATU da 


-ZAHRA'U. Sannan yace, 


KUN SAN WANNE ABU NE YA FASSARA FADIMATU? Nace, bani labari yaa shugabana. Yace; 


AN TSERATAR DA ITA NE DAGA SHARRI. Yace, sa'an nan yace; 


BA DON DAI SHUGABAN MUMINAI (A. S) YA AURETA BA, TO, DA BATA DA ABOKIN HADI A DORON QASA HAR RANAR ALQIYAMA , ADAMU NE KO WANINSA !"



كتاب دلائل الإمامة للطبري، عن الحسن بن أحمد العلوي عن الصدوق‏ مثله بيان يمكن أن يستدل به على كون علي و فاطمة ع أشرف من سائر


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏43، ص: 11


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


08137925034-0812638547


19th Sep, 2020/ 2nd Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post