Daga Kyawawan Dabi'un Annabi Ibrahim (A.S)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


AUNA SU DANA SAYYID ZAKZAKY (H) KA GANI 


Allah (T) ya yiwa Ibrahim (A. S) kyakkyawar shaida wanda hakan yasa ya zama babban abin koyi gare mu. 


Ga shaidar nan kai tsaye daga Allah !


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


الآيات آل عمران‏ فَاتَّبِعُوا مِلَّةَ إِبْراهِيمَ حَنِيفاً وَ ما كانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ‏


" KUMA KU BI TAFARKIN IBRAHIMA MAI KARKATA ZUWA KAN GASKIYA, KUMA BAI KASANCE CIKIN MASU SHIRKA BA ."


 و قال تعالى‏ يا أَهْلَ الْكِتابِ لِمَ تُحَاجُّونَ فِي إِبْراهِيمَ وَ ما أُنْزِلَتِ التَّوْراةُ وَ الْإِنْجِيلُ إِلَّا مِنْ بَعْدِهِ أَ فَلا تَعْقِلُونَ ها أَنْتُمْ هؤُلاءِ حاجَجْتُمْ فِيما لَكُمْ بِهِ عِلْمٌ فَلِمَ تُحَاجُّونَ فِيما لَيْسَ لَكُمْ بِهِ عِلْمٌ وَ اللَّهُ يَعْلَمُ وَ أَنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ ما كانَ إِبْراهِيمُ يَهُودِيًّا وَ لا نَصْرانِيًّا وَ لكِنْ كانَ حَنِيفاً مُسْلِماً وَ ما كانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ إِنَّ أَوْلَى النَّاسِ بِإِبْراهِيمَ لَلَّذِينَ اتَّبَعُوهُ وَ هذَا النَّبِيُّ وَ الَّذِينَ آمَنُوا وَ اللَّهُ وَلِيُّ الْمُؤْمِنِينَ‏[1]


" YAA KU MUTANEN LITTAFI ! DON MENENE KUKE YIN JAYAYYA CIKIN (Al'amarin) IBRAHIM DA MA ABINDA ATTAURA DA INJILA SUKA SAUKAR DA SHI , FACE DAGA BAYANSA , SHIN, BA ZA KU HANKALTA (da abinda ake nuna muku ba) ?"


GA KU YAA WADANNAN (Yahudu da Nasara) KUNYI JAYAYYA CIKIN ABINDA KUKE DA ILIMI, TO, DON MEYE (kuma) ZA KUYI JAYAYYA CIKIN ABINDA BA KU DA ILIMINSA ? ALLAH YA SANI, (alkali) KU KUWA BA KU SANI BA. 


SHI FA IBRAHIM BAI KASANCE BAYAHUDE KO BANASARE BA, SHI DAI MUSULMI NE MAI KARKATA ZUWA KAN GASKIYA , KUMA BAI KASANCE DAGA MASU SHIRKA BA. 


LALLE WANDA YA FI CANCANTA GA IBRAHIM DAGA CIKIN MUTANE SHINE WANDA YA BI SHI (a aiki) DA KUMA WANNAN ANNABIN (Muhammad (S. A. W. W) DA WADANDA SU KAYI IMANI. LALLE ALLAH (fa) MAJIBINCIN (al'amarin) MUMINAI NE (ko ba kwa so) !"




 النساء وَ مَنْ أَحْسَنُ دِيناً مِمَّنْ أَسْلَمَ وَجْهَهُ لِلَّهِ وَ هُوَ مُحْسِنٌ وَ اتَّبَعَ مِلَّةَ إِبْراهِيمَ حَنِيفاً وَ اتَّخَذَ اللَّهُ إِبْراهِيمَ خَلِيلًا


" WAI WA YAFI KYAWUN ADDINI NE FIYE DA WANDA YA MIQA AL'AMARINSA (kwaco-kwaf) ZUWA GA ALLAH KUMA YANA KYAUTATAWA (cikin komai nasa ), SANNAN YA BI TAFARKIN IBRAHIM (daga qarya) ZUWA GASKIYA? KUMA ALLAH YA RIQI IBRAHIM BADADINI (gare shi) !"



 النحل‏ إِنَّ إِبْراهِيمَ كانَ أُمَّةً قانِتاً لِلَّهِ حَنِيفاً وَ لَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ شاكِراً لِأَنْعُمِهِ اجْتَباهُ وَ هَداهُ إِلى‏ صِراطٍ مُسْتَقِيمٍ وَ آتَيْناهُ فِي الدُّنْيا حَسَنَةً وَ إِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ ثُمَّ أَوْحَيْنا إِلَيْكَ أَنِ اتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْراهِيمَ حَنِيفاً وَ ما كانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ‏


" LALLE IBRAHIM (shi kadai) YA KASANCE WATA AL'UMMA MAI QANQAN DA KAI GA ALLAH, MAI KARKATA ZUWA KAN GASKIYA, KUMA BAI KASANCE DAGA MUSHIRIKAI BA. 


MAI GODIYA GAME DA NI'IMOMINSA (wadanda Allah ya yi masa) YA ZABE SHI KUMA YA SHIRYAR DA SHI ZUWA TAFARKI MADAIDAICI. 


KUMA (Allah) YA BA SHI KYAWAWA NA DUNIYA, KUMA SHI A LAHIRA YANA DAGA CIKIN SALIHAI. 


SANNAN MU KAYI WAHAYI ZUWA GARE KA(Yaa Muhammad (S. A. W. W) da ma dukkan wanda yayi imani da kai) CEWA KA BI TAFIRKIN IBRAHIM MAI KARKATA ZUWA KAN GASKIYA , SHI BAI KASANCE DAGA MASU YIN SHIRKA (cikin bautar wadanda suka saba maka ba) ."



 تفسير قال الطبرسي رحمه الله في قوله تعالى‏ لِمَ تُحَاجُّونَ‏ قال ابن عباس و غيره إن أحبار اليهود و نصارى نجران اجتمعوا عند رسول الله ص فتنازعوا في إبراهيم‏


__________________________-

(1) هكذا في النسخ و الترتيب يقتضى تقدم الآيات على قوله: «فَاتَّبِعُوا مِلَّةَ إِبْراهِيمَ».


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏12، ص: 2


Wa kaga ya siffantu da wadannan ayoyi in ba Sayyid Zakzaky (H) ba? 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

         (08137925034)


20th Sep, 2020/ 3rd Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post