Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai Ya Huce Haushin Sa Akan Ƴan Shi'a

 




Zaharaddeen Mziag

Duk da ba bakon abu bane ga mu 'yan shi'a mabiya jagora Sheikh Ibraheem yaqub El'zakzaky, kisa kamu da ɗauri'amma munsan a runa wai ansaci zanen uwar El'rufa'i.

 Abinda ya faru na dakatar da Gwamnan kaduna Nasiru el'rufa'i daga babban taron ƙungiyar lauyoyi wato NBA wanda El'rufa'i yaji takaici sosai wanda har yake faɗima makusantan sa cewa ƙungiyar Elzakzaky tana fallasa shi da ƙara jawo masa baƙin jini a duniya. 

Da yake shi wawa ne hasali ma bai dauki ran ɗan adam bakin komai ba shiyasa ya ƙara daɓama kansa wuka ta hanyar sake afkama raunana 'yan shi'a da kisa a daidai lokacin da suke gudanar da zaman juyayin ashura na bana a kaduna. 

Ya manta da cewa wan'nan rashin imanin da yake da kuma ko in kula game da rikicin kudancin kaduna na ɗaya daga cikin abinda yasanya ƙungiyar lauyoyi ta NBA ta ga rashin cancantar sa da zama ɗaya daga cikin masu gabatar da jawabi a babban taron. 

Kungiyar Lauyoyi sunyi nazari mai zurfi dangane da wanene Nasiru El'rufa'a, Kuma sungano shi mutum ne mugu mara imani, kuma mutum ne mai matuƙar son kansa. 

Nasiru El'rufa'i mutum ne mai butulci mara amana kuma maƙaryaci da raina mutane, kuma idan yana gaba da kai ko yana jin haushin ka zai iya ɓatar da kai kamar yanda ake zargin yayi ma wani malamin jami'a da yayi ƙaurin suna wajen fallasa Gwamnatin sa. 

Wanda keda irin wan'nan halin lallai bai cancanci zama shugaban al'uma ba amma dayake ɗan Nigeria mantuwa gare shi, sai gashi ya zaɓi maƙiyin sa domin ya jagorance shi. 

Ko shakka babu na daga cikin wan'nan ɗabi'ar ko ince mugun halin yasanya ƙungiyar lauyoyi ta jefar dashi daga cikin amintattun da zasu gabatar da jawabi a wajen taron. 

Kungiyar lauyoyi kungiya ce da tasan doka ta karanci doka kuma take binta sau da ƙafa, ƙungiya ce da mafi yawa daga cikin su masu fafutukar adalci ne da kuma dawo da doka. 

Nasiru El'rufa'i yayi ƙaurin suna wajen take doka da kama ƙarya da raina kotu. 

In ba haka ba yau kusan shekara hudu da wata Babbar kotu a abuja ta bada umarnin asaki jagoran mu Malam Zakzaky kuma biyashi diyya ta miliyan hamsin a gina masa gida duk inda yakeso a arewacin Nigeria amma Nasiru el'rufa'i da Gwamnatin sa sunyi ko oho da wan'nan hukuncin, sai ma ƙara kashe ma malam Zakzaky mabiya sukeyi 

Don raina doka da rashin kunya sai kuma ya sake shigar da wata ƙarar a cikin jihar sa tsawon shekaru ana shari'a amma haryanzu sunkasa kawo wata gamsasshiyar sheda akan abinda suke zargin malam zakzaky da aikatawa, alhali kuma su kullum suna aikata mafi munin abinda suke zargin malam zakzaky da dashi. 

Abinda zamuce maka Nasiru El'rufa'i shine kaci talatar ka kafin larabar ka tazo, wallahi abinda kuke mana zamu rama. 

Idan giyar mulki ta mantar da kai katuna cewa saura shekara biyu da wata bakwai ku sauka, don haka ka ƙara himma wajen rashin imanin ka akan 'yan shi'a nasan koda kullum kake kashe mutum goma daga cikin mu, to zaka sauka ka barmu daram. 

Zakaga munayi bamu fasa ba a lokacin da baka sawa baka hanawa, kuma zamu sanya maka ido wallahi sai munga bayanka. 

Kuma muna ƙara jaddada goyon bayan mu ga ƙungiyar lauyoyi, lallai sun kyauta sunyi abin a yaba sun nuna ma duniya cewa su kungiya ce da take bin doka kuma take tare da masu bin doka ba irin su Kare el'rufa'i ba. Idan shine ya baka haushi mun ƙara kisa kuma kada ka fasa.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post