Ba ka Raba 'Dan Nigeria da Aikin Banza !!!



 MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES

Wannan qasa tamu Nigeria qasa ce wacce take cike da jama'ah masu karatu, wayewa da neman kudi, amma duk da irin wannan abinda ta tara, sakamakon rashin tarbiyyar da ta rasa sai kuma suka 'yancin tunani kwata-kwata !

A qalla muna gaf da cika shekaru 4 kenan da kafuwar sabuwar Gwamnati wacce ake mata fatan samun canji daga gare ta.
Ba zan ce an rasa canji ba, domin ko ba komai an sami canjin shugabanni wadanda suka canza rayuwarsu da rayuwar 'ya'yansu da matansu, amma ba rayuwar wadanda suka zabe su ba.

Na'am, ta bangaren wadanda su kayi zabe su ma ba su rasa wani abu ba, domin an jefa su cikin quncin rayuwa ta hanyar yunwatar dasu da kuma karkashe musu mata, mazaje da kuma 'ya'ya.

Masu kiran kansu da sunan malunta sun taka rawar gani wajen gurbata tarbiyyar 'yan Nigeria ta hanyar cusa musu qiyayyar masu t
riqo da addini, tare da cusa musu soyayyar masu cutar da su. Wannan dalili yasa mafi yawan 'yan Nigeria ba su da tunanin kansu, sun ginu ne akwai bisa tunanin wasu masu yin tunani don neman biyan buqatun duniyarsu.

Guguwar siyasa ta kada cikin wannan sati wacce ke gwara kawukan jama'a masu tafiya cikin jam'iyya iri daya. Salon da jam'iyya me ta dauka na kama-karya ya zama iri daya dana Gwamnatin da ta shude. Har kaji suna cewa;
" DAMA MUTUM 'DAYA NE CIKIN JAM'IYYAR NAN MAI GASKIYA, RIQON AMANA DA TAUSAYIN TALAKAWA (wato BUHARI) ."
Amma in ka tambaye su da su kawo maka abu guda daya rak na cigaba da yayi wanda ke nuna tausayawa talakawa sai kaji suna cewa;
" KU SAURARA ZUWA WANNAN ZAGAYE NA BIYU (second tanure) ko Next Level,K GANI, DOMIN AKWAI KYAWAWAN MANUFA CIKE CIKIN ZUCIYARSA ." to Gashi Amma Sai Munana Muke Gani. Amma Dai Ga Waninan Yana Zaman Saurare Har yanzu ko Bukatarsa Zata Biya??

Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034-08126385470).

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post