ABIN TAKAICI, SOYAYYAR YAUDARA CIKIN 'YAN'UWA !!!


MA'ASUMIYAH NIGERIAN NEWS UPDATES
Shi so wani abu ne da Allah (T) ke kimsa shi cikin zuciyar dan Adam sakamakon gani ko kuma magana (verbal exchange).
Gani kan kasance ne yayin haduwa da juna (physical contact), amma magana na samuwa ne ta hanyoyi biyu, wato waya (phone) ko kuma yanar Gizo (social media) wanda za a riqa rubutawa juna saqo (text message).

Abinda ya kamata ga mutum musamman dan gwagwarmaya yayi shine, idan suka hadu ta wadannan hanyoyi sai son juna ko son daya daga cikinsu ya shiga zuciyar daya har ta kai aka furta shi, to, shi wanda aka furtawa yayi nazarin yiwuwar wannan al'amari da kyau.

Idan yaga ba mai yiwuwa bane saboda wasu dalilai nasa , to sai ya yiwa abokin nasa bayani cikin hikima ta yadda ba zai dizga/kunyata abokin nasa ba, hakan zai iya kawo dorewar mutumci tsakaninsu.
Abinda kasan ba ka so ayi ma shi, to, bai kamata ace Kai ka yiwa wani ba, domin abinda kayi kaima za ayi maka shi.
Abin takaicin shine, brother ne zai iya furtawa sister cewa yana sonta da gaske, amma cikin zuciyarsa yaudara ce. Ya riqe ta ne kawai a matsayin me debe masa kewa lokacin da yaso.

Hakama ana samu cikin sisters wacce za ta nuna tana son mutum alhali ba da gaske bane cikin zuciyarta. Tana iya yiwuwa ma a wannan lokaci tana da ranar aurenta a kanta ko kuma akwai wani alqawari da wani.

A gaskiya wannan dabi'a ce wacce ta sabawa koyarwar jagoranmu, kuma tayi hannun Riga da tarbiyyar harka.
IDAN KASAN BA ZA KA AURI YARINYA BA, TO, KADA KA FURTA KALMAR SO GARE TA.
Daga wakilanmu na Bauchi Zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034-08126385470).
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post