LIKITA-Miyasa Maniyyi Na Yake Tsinkewa (Katsewa) Yazama Kamar Ruwa ??


MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATED

Alkalamin:Arrida Chemist💊Shinkafi

Tsinkewar maniyyi yakanzo ne sanadiyar abubuwa da dama na samun canjin abincin da Dan Adam yakeci da rashin samun isashen abinci me Gina jiki Amman bacutabace ke haddasashi ba, Kuma ba ciwo bane.

1. Ballema idan cuta tashiga cikin maniyyi to baya tsinkewar sedai yayi kauri wato yazama kitif- kitif kamar kunu sanadiyar bayyanar kwayoyin cutar bacteria wadda muke cema cutar infection kokuma cutar sanyin ga maza da Mata Wanda alamomine idan macce ko namiji yaje fitsari bayan Gama fitsarin zega fararen ruwa suna biyowa baya wannan shine cuta ke haddasawa.


TSINKEWAR maniyyi '''' abune dake faruwa sanadiyar rashin isashen abinci me Gina jiki ya danganta ne daga canzawar abinci da kuma rashin samun abinci me Gina jiki kamar kana Zamfara seka koma kano idan kasamu canjin abinci to maniyyin ka ze iya tsinkewa a lokacin sanadiyar samun canjin abinci, abunda yake karama maniyyin lafiya da karfi sannan da lafiyar jiki sune:

1.milk Madara
2.kifi
3.nama
4.lemu
5.kankana
6.meat nama
7.kunun Aya
da sauransu

sannan tsinkaken maniyyi idan aka sadu da macce yana samar da ciki wato juna biyu Babu wata matsala, Don mutun yaga kanshi da tsinkakken maniyyi kawai canjin yanayin abinci da rashin samun abinci me Gina jiki yake kawo hakan,

sannan Kuma akwai maziyyi Wanda shi ruwane sanadiyar yar karamar Sha' awa yake fitoma Mata da maza wannan dama shi bayada kauri, Amman Wanda ke fitowa lokacin Jima' i shine maniyyi.

Allah ya kara kwazo

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post