Buhari Shugaban Ƙasa ko shugaban Masu kisa??



Tarihi kullum maimaita kan sa yake, in muka kalli abin da wadannan azzalumai @Mbuhari Da @Elrufa'i suke a wannan ƙasa. To, zaluncin su ya fice na zamanin fir'auna. Kada mu manta sabida ciyar wa da Fir'auna yake yiwa al'ummar sa ne, har Allah ya tsawaita ran sa a duniya, yana rage wa daga adadin abincin da yake bada wa Allah na rage wa daga kwanakin sa.

Amma yanzun masu mulkin wannan ƙasa babu ta yadda ba hankoron kisa suke ba, in basu bada umurni n harbe ka da bindiga ba zasu kashe ka da yunwa da talauci. Bugu da ƙari kuma yaran su kullum fatautar ran ka suke. Da sunar wata tsita wai Boko-haram.

Burin talaka da fatan su kullum akan ku yake, amma ba kwa da wata fata sai na ganin basu wanzuwa a doron ƙasa, shin, idan babu su nan gaba wa zaku mulka, kun yarda a kashe al'ummar ku a baku kuɗi, kuɗi masu karewa anan duniya! Kun barranta da neman dacewa a lahirar ku?

Koda yake ma, ku baku san lahirar ba, don ayyukan ku ya nuna baku yarda da za'a tashi a koma ga Allah wata rana ba, babu wanda zaiyi Imani, ya kuma yarda da ranar lahira da tashin ƙabari face ya kiyaye duk wani abu da zai zama barazana ga lahirar ga jin daɗin sa a lahira.

Amma ku duniya kawai kuka saka a gaba, ku kashe ku bisne, ku kuma fito da sunan ku zakuyi gyara akan aikin da kune ke aikata wa. Wannan wawancin da rainin wayon ya isa haka nan. Domin abinda kuke kullum ƙara tona wa kan ku asiri kuke.

Yau da yin waƙi'ar Zaria kimanin shekaru biyar, kuma kullum ƙara karkashe al'umma kuke, wanna ya isa hujjah duniya ta juya muku baya, duk da cewar makahon son da mabiyan ku ke muku wasu lokutan yakan sa su kasa ganin laifin ku, amma yanzu fa??

Wallahi da in ka fito kana zagin waɗannan azzalamai, wani sai ya kafirta ka, ko ya halasta jinin ka, amma yanzu tsinuwa da la'antar azzalumai ya zama wazifar ko wanni dan Najeriya. To, wannan lallai, bai isa ba, dole abinda muke ji a zuciyoyin mu, mu fitar dashi fili, mu yishi a aikace, muce mu baza mu biye wa mulkin zalun ci ba, addinin Allah muke so yayi iko damu koda kuwa zamu rasa rayukan mu, duk da nasan ba zai yiwu a kashe mu baki daya ba, wasu ne zasu bada jini domin dukkan mu mu sani ƴanci.

Wannan kawai shine mafita, kuma shine kiran da Malam El-Zakzaky (H) yake yi tsawon shekaru Arba'in, kuma wannan shine zai saka mana ƴanci da aminci a cikin al'ummar mu, ya zama kuma tsira a lahirar mu.

Zakzaky yayi wannan kira ne na bara'a ga zalunci da tabbatar da adalci yasa azzalumai suke farautar sa tsawon shekaru talatin da tara (39), sun kamashi wajen sau 9, a wannan na karshen ne suka kashe mabiyan sa mutum 1000 da wani abu, wanda ya haɗa, mata, maza, mata masu ciki, jarirai harda ma tsofaffi.

Wannan ya kara tabbatar mana da lallai, muna kan daidai, domin ba wanda za'a jarabce shi da irin wannan jarabawar sai, magajin Annabawa, mai kira zuwa ga addinin Allah, domin sunnar su ce Wannan, muzguna wa, kisa da ɗauri.

A ƙarshe ina jaddada kira ga Gwamnatin Zalunci da ta Gaggauta sako mana Jagoran mu, ba bisa sharadi ba. Allah ya kwato mana jagoran mu Sayyid Zakzaky, ya bashi lafiya da nisan kwana.

Daga Wakilan Mu Na Saminaka
      Tare da
Bin Haroun Sigau

#JusticeForZakzaky
#FreedomForZakzaky

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post