Wanene Jarumi Zuhair Bin Qain??



Sunansa: ZUHAIR BIN QAIN bin qais al-ammary al-bajliyyu asalinsa dan wata babbar qalilane datake a garin (KUFA) kasar IRAQ yakasance mutumne mae matukar daukaka a kabilarsu jarumin gaskene.

Mahaifinsa: QAIN yakasance sahabin annabine mae matukar biyayya gareshi ZUHAIR yanadaga cikin manyan mataemaka imam husain(as) a filin karbala gashi babban jarumine a rundunar sahabban imam.

ZUHAIR KAFIN WAKI"AR KARBALA.
   An ruwaito daga daya daga cikin makusantan zuhair yana cewa" mun kasance tare da zuhair bin qain lokacin dawowarsa daga makkah aikin hajji munnufi hanyarmu takomawa kasar iraq sae muka hangi imam husain(as) da rundunarsa suna tafiya, a lokacin kuma shi zuhair yanajin kunyar su hadu da imam" a masauki katsam muna tsaka da tafiya sai muka hangi imam(as) sun yada zango a gabanmu, sae muma muka yada zango kusa da imam" sae imam husain(as) ya tashi dan aike zuwa gurin zuhair bin qain, dan sako yana isa gurin zuhair yace masa YA ZUHAIR" imam yana kiranka zuwa gareshi sai zuhair yayi shiru sabida kunyar imam(as) dalili kuwa shine shi zuhair yakasance dan QABILAR (USMANIYYANE) sai matar ZUHAIR tayi kokarin karfafashi dazuwa kiran IMAM(as) tace masa imam husaini ne yake kiranka dan fadima(s) jikan manzo Allah(s.a.w) daga ya dau azama da zuwa kiran IMAM" zuhair yana zuwa gun IMAM " bai dadeba yadawo cikin farinciki fuskarsa cikin murmushi da annushuwa, daya karaso gurin mutanensa yace masu to mae yake da kwadayin yatafi dani yazo muje domin taemakon imam" a filin karbala, sai ya kira matarsa cikin kyakkyawar fuska tare murmushi mai sanya farinciki yace mata nasakeki dominni zanje nayi shahada tare da imam husain (as) sai bata dukiya mae yawa yace mata tabi dan uwanta taje tayi sallah a gidanta dominni nasadaukar da rayuwata zuwa jikan shugaban halitta (s).
Sai yakara cema sahabbansa wanda yakeso yabini yazo muje domin wannan itace ranar alkawarina karshe, sai yace" zan fadimaku wata magana yakinmu zae kasance cikin qishirwa wanda Allah, yayimana busharar cewa zai jarabbcemu' sai wani daga daga cikin sahabbansa mae suna salmanu (albahili) yace shin kuna farinciki da abinda da Allah ya bayyana maku ? kuma kuna murna da wannan sai zuhair yace masa na"am, sai yace idan kuka tarar da matasan iyalan gidan annabi(s.a.w) kukasance masu taemakonsu da abinda da Allah ya wadataku dashi, amma kumani zan nemomusu taemakon Allah "

Daganan zuhair bin qain yayi shiri zuwa gurin imam" tare da ga dan uwan mahaifinsa wanda ake cemasa (salmanu bin mudarib).

ZUHAI BIN QAIN A FILIN KARBALA.

Ranar (9) ga watan muharram lokacin da ibn sa'ad (l.a) ya tashi ya nufi rundunar imam husain(a's) a daren alkhamis yayi kiran rundunar mayaqa dasu nufi wajen jikan manzon Allah(s.aw) Shi kuma zuhair yana zaune a cikin rundunar imam" yana riqe da takobinsa sai imam" yace umarci dan uwansa abal fadl abbas yace masa jeka kaji wadannan mai yake tafe dasu? sai abal fadl ya shirya jaruman gaske aqallah mutum (20) yanufi wajen makiya dasu, daga cikinsu akwai habib bin muzahir da zuhair bin qain ...

Zuhair yakasance jarumin gaske yana daya daga cikin wandanda suka hakura da jindadin duniya suke da shauqin komawa ga mahaliccinsu a karkashin taemakon imam husain a filin karbala, jarumi zuhair yayi kirari wa kansa yana mae jindadin kasancewarsa tare da imam" na fuskantar rundunar yazeedu(l.a) makiya Allah da manzonsa, jarumi zuhair ya nufi mayakan batare da tsoroba, yana mae azamar riskar shahada yashiga sansanin mayaqa bayan sun jawo hankalin rundunar ibn sa'ad akan cewa yanzu wacce asarace zata sanyasu suyaqi imami dan imami jinkan rahamar halittu annabi muhmmad(s.a.w) rundunar yazeedu sukayi burus da nasihar da ake masu, suka shigo suna sara zuhair jarumi tare da wasu sahabban imam" suka fuskanci makiya Allah, suna masu kabbara masu shauqin shahada zuhair yayi shahada a ranar (10) ga watan muharram yana mae shaukin haduwa da rahamar Allah.

Amincin Allah da yardansa su tabbabta gareka ya ZUHAIR BIN QAIN shahadar takasance cikin daukaka tafarkin Allah(s).

A takaice kenan
wasslamu alaikum.


Bin Ishaq aliyu gano.
Email:kamarizzaddeen36@gmail.com.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post