Duk Wanda Ya Zaɓi Lahirar Sa, Zai Cutu A Duniyar Sa!





@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @

KA FIFITA ABINDA KE WANZUWAKAN ABINDA YAKE QAREWA

Al'ummar Manzon Allah (S.A.W.W)ta wannan zamani ta fada halaka ta hanyar fifita rayuwar duniya.

Duk wani abinda kake gani ake aikatawa na sabo ko kangarewa Allah, to, hakan na faruwa ne sakamakon fifita duniya. Fifito duniya ne yasa ake tsafe-tsafe don neman mulki, ko kuma biyayya ga azzalumai don samun karbuwa a wajensu, ko kuma dai aikata dukkan miyagun ayyuka da aka hane mu aikata su.

Saboda sun san ba su da gida (na rahma)a lahira yasa suka maida duniya ta zama gida gare su, alhali wannan gida ba mai aminci bane.

Ga wasu hadisai guda biyu wadanda suke mana nuni game da matsayin rayuwarmu.

Manzon Allah (S.A.W.W)yana cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ ITA DUNIYA GIDA CE TA WANDA BA SHI DA GIDA (a lahira), KUMA DUKIYAR WANDA BA SHI DA DUKIYA (arziqin lahira), KUMA GARE TA NE MARAR HANKALI KE TARAWA (maimakon tara ayyukan alkhairi).‘’

A wani hadisin kuma ya qara da cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ DUK WANDA KE SON DUNIYA ZAI CUTU DA LAHIRARSA, KUMA DUK WANDA KE SON LAHIRARSA TO ZAI CUTU DA DUNIYARSA. KU FIFITA ABINDA KE WANZUWA KAN ABINDA KE QAREWA .‘’

(Musnad Ahmad, J:4, SH:412).

Da fatan za a dau darasi cikin wannan tunatarwa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~5th May, 2020.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post