Kuji Tsoron Duniya, Kuma Kuji Tsoron Mata!!!






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ALLAH YA SANYA MU KHALIFOFI NE A DORON QASA

Duk wanda ka ganshi a doron qasa khalifan Allah ne da ya sanya shi don yimar wani aiki wanda sai an je lahira za a duba wannan aiki nasa a gani, shin, yayi da kyau ko ya munana shi?

Kowa kan yi abinda yaga dama, amma Allah na barinsa ne ba don ya fi qarfinsa ba, sai dai kawai albarkacin addu'ar Annabi (S.A.W.W )wacce yayi mana don a jirkirtawa kowa aikinsa sai an je lahira.

Amma Allah ya kawo mana qissosin magabata wadanda suka kangare masa, da kuma yadda akayi da su don mu dau darasi daga gare su.

Allah (T )ya bamu labari kamar haka:

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Haqiqa mun halakar da qarnoni (masu yawa )gabaninku yayin da su kayi zalunci (ta hanyar danne haqqoqin junansu da kuma shirka ), kuma Manzanninsu sun je musu da hujjoji (bayyanannu )amma ba su kasance masu yin imani (da su ) ba , kamar haka muke sakawa mutane kangararru.

Sa'an nan muka sanya ku khalifofi a doron qasa a bayansu don muga yadda (ku ma )za ku aikata .‘’

(Suratul-Yunus, aya ta 13-14)

Ba wani abu ne ya sa su wannan kangarewar ba sai tsananin son duniya da jin dadinta, alhali ita duniya rudi ne da ita.

Manzon Allah (S.A.W.W )ya tsoratar damu kan abubuwa biyu masu saurin halakarwa cikin wannan hadisi da ke tafe cewa:

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Lalle ita duniya fure (flower ) ce kore , kuma lalle Allah mai khalifantar da ku ne a cikinta kuma (don )yaga ku ma ya za aikata . Ku ji tsoron duniya kuma ku ji tsoron (sharri da makircin )mata, domin farkon fitinar (da aka jarrabi )Banu-Isra'ila (da ita )ta kasance mata ne .‘’

(Muslim , J:7, SH:89)

To, yanzu muma mun fada cikin wannan fitina ta mata 👨🏻‍🚀🤓🤶🏻, domin yawancin halakar da maza ke yi a wannan zamani sanadinsu ne.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

~29th May, 2020/ 8-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post