Fifikon Nana Khadijah (S.A) Akan Sauran Matan Annabi (S.A.W.W) !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YADDA ALLAH YA FIFITA ANNABI (S.A.W.W )KAN SAURAN ANNABAWA HAKA YA FIFITATA A KANSU

‘’ Wadancan manzanni ne , mun fifita sashensu akan sashe.‘’ inji Allah , kuma kamar haka Allah ya fifita Khadijah (S.A )akan sauran matan Annabi (S.A.W.W ).

Duk wanda kaga Allah ya fifita matsayinsa kan sauran mutane , to, ya yi hakan ne bisa cancanta ba wai don nuna bambanci ba, domin Shi Allah ba a tambayarsa kan cewa me yasa yayi haka .

Duk da cewa babu inganci cikin maganar , amma dai an kawo sunayen wasu mutane 10 wadanda ake cewa wai anyi musu bushara da Aljannah .

A iya tunaninmu na 'yan adam za muga cewa ai in kusanci na sa a yiwa mutum busharar Aljannah tun daga duniya, to, ya kamata ace matan fiyayyen halitta (S.A.W.W )sun sami kansu ciki.

Sai dai abin mamaki ko hadisi mai rauni (DHA'IFI )ba a kawo cewa akwai wata mace daga cikinsu wacce aka yi mata wannan bushara ba in har ka cire Sayyidah Khadijah (S.A ).

Ya tabbata cikin Bukhari da Muslim cewa, Annabi (S.A.W.W )yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ LALLE ALLAH YA UMARCE NI DA NA YIWA KHADIJAH BUSHARA DA WANI GIDA A ALJANNAH NA BENI (upstair), BABU QUNCI A CIKINSA, KUMA BABU WAHALA.‘’

- Bukhari , J:3, SH:7.

- Muslim , J:7, SH:133.

Wannan matsayi nata yasa har ta bar duniya ba ayi mata kishiya ba, kuma ya cigaba da yabonta da kyautatawa qawayenta bayan ranta. Har wata rana ummul-muminina A'isha ta nuna bacin ranta game da abinda Annabi (S.A.W.W )ke yi na ambaton sunanta (Khadijah ), alhali Shi ba a zarginsa cikin komai nasa.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~26th May, 2020/ 5-10-1441.

  KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post