Dandalin Matasan Harka Islamiyya Ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Zakzaky (H) Na Garin Bauchi Da Kewaye Sun Kai Ziyarar Sallah Ga Wakilin Ƴan Uwa Hujjatul Islam Sheikh Adamu Tsoho Jos



ZIYARA! ZIYARA!! ZIYARA!!!.

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

~Dandalin Matasan Harkar musulunci a Nijeria, Karkashin jagoranchin maulana sayeed Ibrahim Yaqoub El-zakzaky (H) na Garin Bauchi da Kewayenta Sun kai ziyara ga Hjjatul islam wal muslimin, Sheikh Adamu Tsoho Ahmad jos, Tareda ziyarar dandalin matasa na Jos Domin kara Kulla alaka a Tsakani matasan Gari Biyun.

~cikin jawaban da Su sheikh suka Mana.
Da Farko sun mana magana ne akan Tasirin Ramadan ga yan uwa, Bayan Gama Azumin watan Ramadan, Akalla wata shida Yazama Ramadan yana tasiri a Jikin mutum wato Rabin shekara, sauran wata shidar kuma Shirye-shiryen Ramadan mai Zuwa.

~Na Biyu Yayi magana akan Muhimmancin Neman Ilimi don Bada Gudumuwwa Ga Dukkan Bangaren Da Mutum ya Kware, da Kuma Nuna Muhimmancin Samartaka, wajen yin Amfani da Wannan Dama Don kama Hanyar da Mutum keso ya cimma a Wannan Harka Islamiyya.

~ na Uku yayi magana akan Hadafin ita wannan Gwagwarmaya, sanin Hadafin Harka shidai sa Mutum ya Kaucewa Aikata duk wani Abunda Bai Hadafin Harka Ba, misali: fada Da Junanmu koh Gaba.

Wannan shine Takaitaccen Jawabin da Shi Sheihin Malamin ya mana A Ziyara da Muka Kai masa Jiya a Husainiyyatu zakzaky Jos.

~~ Haidar Aliyu Alkaleri.
A Madadin Dandalin matasan Bauchi da Kewaye.






Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post