Da Hannun Malamai Cikin Wannan Fitinar Data Addabi Qasa!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

SUNA DA IKON YIN MAGANA AMMA SUKA KAME BAKUNANSU

Hausawa na yin wata karin magana da cewa, ‘’ WANDA YA QI JI BA ZAI QI GANI BA !‘’ Da gaske wannan magana haka take, domin an qi jin kiran Allah, ga shi kuma ana ganin abinda zuciya ba ta so .

Laifin maluma ne musabbabin fadawarmu cikin wannan hali da kowa ke kokawa, da sun dau mataki da bamu sami kanmu cikin haka ba.


Wasu tsiraru sun fusata Allah ta hanyar aikata mafi munin zunufi wanda hakan yayi sanadin fadawar dukkan al'umma cikin musifa sakamakon goyon bayan da miyagun maluma su kayi.

Ya tabbata cikin hadisan Ma'aiki (S.A.W.W )cewa matuqar za a riqa aikata munanan ayyuka ana yin shiru ba tare da inkarin wannan abu ba, to, za mu fada cikin bala'i wanda addu'armu ba za ta amfane mu ba.

GA HADISAN KAMAR HAKA:-

(1)- ‘’ Lalle Allah mai girma da daukaka ba ya azabtar da dukkan al'umma baki daya saboda ayyukan tsiraru (few of them )har sai sunga ana aikata mummuna aiki a tsakaninsu kuma suna da ikon (fitowa suyi magana don )hanawa amma sun qi qyamatarsa (sai goyon baya ), to, idan suka aikata haka sai Allah ya azabtar da (wadannan )tsiraru da kuma (dukkan )al'umma .‘’

 (Musnad Ahmad , J:4, SH:192)

(2)- ‘’ Na rantse da wanda raina ke hannunsa (Allah ), ko dai ku riqa yin umarni da (aikata )kyakkyawa da kuma yin hani (ga aikata )mummuna , ko kuma Allah ya yi kusa ya aiko da azaba a kanku daga gare Shi, sa'an nan kuyi ta roqonsa (addu'a )kuma ya qi amsa muku.‘’

A wata riwayar kuma yace;‘’ KO KUMA YA 'DORA WATA JAMA'A (azzaluma )A KANKU, SA'AN KUYI TA ROQONSA KUMA BA ZAI AMSA MUKU BA.‘’

(Musnad Ahmad , J:5, SH:388)

Yanzu ba irin nau'in zalunci da ba a yi, amma maimako malamai su nuna qyamatar hakan sai fitowa suke yi suna goyon baya don neman duniya .

Da ma Allah (T )ya riga ya fada mana cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ KU JI TSORON FITINA WACCE BA IYA KAN WADANDA SUKA AIKATA ZALUNCI TAKE TSAYAWA BA , KUMA KU SANI LALLE ALLAH MAI TSANANIN UQUBA NE .‘’

(Anfal, aya ta 25)

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

      09039791509

~25th May, 2020/ 4-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post