Ɓataccen Jagora Na Ɗauke Da Misalin Laifin Dukkan Waɗanda Suka Bishi!!!




@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @

KADA NEMAN JAGORANCI YA RUDE KA WAJEN BATAR DA JAMA'AH

Abin mamaki shine, akwai wasu jinsin mutane wadanda son shugabanci ya mamaye zukatansu ta yadda ko su biyu ne suke tafiya sai sun ji cikin zuciyarsu cewa ina ma ace sune shugabanni cikin wannan tafiya , kuma yawancin irin wadannan mutane an fi samunsu cikin addini izala .

In abin ace an ba ka (assignment )ne sai nace kowa ya lura da wannan matuqar mu'amala ta hada shi da dan addinin izala , zai ga cewa ya fi so ace shine jagora kan komai .

Rashin sanin illar wannan abu yasa da zarar wani daga cikinsu yayi karatu ba shi da wani buri face kawai yaga ya samar da jama'ah wadanda za su bi shi .

Saboda haka sai su riqa amfani da ayoyi ko hadisai suna canza ma'anarsu zuwa yadda za su sami mabiya masu ganin babu wani mai karatu kamarsu .

To, ku sani cewa, Annabi (S.A.W.W )na fada cikin wani hadisi kamar haka;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Duk wanda yayi kira zuwa ga shiriya yana da lada misalin ladan dukkan wadanda suka bi shi , ba tare da an tauye wani abu (cikin ladarsu ba ), kuma wanda yayi kira zuwa ga bata yana da misalin zunubin dukkan wadanda suka bi shi (kan wannan bata tasa )ba tare da an tauye wani abu cikin zunubansu ba.‘’

- Sunan Abu Dawud, J:4, SH:201.

- Ibn Majah, J:1, SH:275.

- Musnad ANDROIDhmad , J:2, SH:397.

Wannan hadisi na fassara ayar nan da ke cewa;

‘’ Kuma za su dauki nauyinsu (na zunubi )da wani nauyi (na mabiyansu )tare da nauyinsu, kuma ranar alqiyama za a tambaye su kan abinda suka qirqira(don batar da jama'ah ).‘’

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~25th May, 2020/ 4-10-1441.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post