Iyali A Muslunci.. Fita Na Ɗaya (1)






Auren Wuri...

Rbtw: Bin Haroun Sigau

Da sunan Allah mai murƙushe azzalumai, tsira da aminci su tabbata ga Fiyayyen Halitta da Iyalan gidan sa Tsarkaka.

In Allah ya yarje min, zanyi wasu rubututtuka ne da suka shafi Iyali, da kuma abinda ya shafi zaman aure (Hanyar Samar da iyali) na gari bisa dan abinda ba'a rasa ba.

Shimfiɗa
√√√√√√√

To, shi soyayya wani abu ne da dama hakanan Allah ya gina mu akan sa, ya kuma mayar dashi wani sashi na tafiyar da rayuwar mu baki ɗaya. Ta yadda kowa ka gansa, yazo wannan duniyar ne ta silar SO.

Wannan bazai ɓuya wa kowan nen mu ba, son nan, ta hanyar dalilin zuwar mu duniyar ne ko kuma ta hanyar iyayen mu da suka haifo mu ne.

Duk in muka duba zamu ga so ne dai ainihin silar zuwan mu, badon soyayyar da Allah yake wa Manzon mu ba da bai halicci wannan duniya ba da mu baki ɗaya. Shi kuma Manzon mu, ya zama yafi son mu fiye da kansa. Ta yadda, duk wani abu da Allah ya saukar masa in muka duba zamu ga abinda yake fara tambaya shine al'umma ta!

Ba ƙaramin daraja bane a yika a wannan al'umma, tabbas, inka sami kanka a wannan shima silar so ne da Allah yake maka, don Annabawa baki ɗayan su sun so samun hakan.

To, insha Allah, bari muje kai tasaye zuwa abinda muke son isar wa. Bi Ma'ana Batu kan Auren Wuri.

Shi aure Sunna ce Babba daga cikin sunnar ma'aikin mu (S) wanda har yake cewa da bakin sa mai albarka, "Kuyi aure ku hayayyafa, zanyi alfahari daku ranar alƙiyama".

To, sai ya zamana yanzu muna wani zamani, ko ince wani lokaci, da rayuwa ta lalace, muka lalatar da kanmu, ta hanyar barin kan turbar Manzon Allah (s.a.w.w) na haƙiƙa, muka ɗauki rayuwar maƙiyan mu amsu adawa da addini mu.

Mu koma tarihi mu gani, shin Manzon Allah a wani shekara ya aurar da ɗiyar sa, farin cikin sa Sayyada Zahra (S). Duk da irin son daya ke mata da kuma son kasancewa da ita, sabila da rashin mahifiyar ta Sayyida Khadija (As)!

Hakanan ya aurar da Ita tana kimanin Shekaru tara, a wasu ƙaulin kuma akace; tana gab da cika shekara goma. A tunanin ku, munfi Manzon Allah sanin ya kamata ne?? A'ah ko ɗaya, hasali ma, dukkan wani abu daya aikata, ko yayi umurni da aikata, ko kuma aka aikata a gabansa bai hana ba, wahayi ne daga Allah Masanin kowa da komi.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Domin shi, dukkan komi nasa, umurni ne daga Allah. Ya furta ko bai furta ba. Shiyasa in muka duba ayoyin Alqur'ani baki dayan su dake magana da Manzon Allah zamu ga cewa; qada'an ba suna magana akan sa bane, Allah yana magana dashi ne a maimakon mu.

Domin yazam abin koyin mu, samfurin mu, wanda zamuyi koyi dashi mu tsira gobe ƙiyama. Tabbas, akwai hikima cikin aurar da yara da wuri musamman a wannan yanayi na lalacewar tarbiyya, da shigowar gurɓatattun abubuwa a cikin addini keta faruwa don yaƙar imanin mu cikin ruwan sanyi kullum shine aikin da Yahudawa suka ɗaukar wa kansu.

Yara yanzu ko ɗan shekara biyar, sai kaji yana maganar Soyayya, budurwa, aure da sauran su..
Hakan yana faruwa ne, dalilin abubuwan dake wakana a idon sa yau da kullum.

Rayuwar nan baki ɗayan ta makaranta ce, ka zauna an koya maka ko baka zauna ba, zaka sha ilimummuka kala-kala. Waɗan da suka dace da wanda basu dace ba. Yanzu iyaye sun miƙe ƙafa, su ala dole yara sai sun kai wani matsayi a karatu, ko sun fara aiki kana za'ai masu aure.

A lokaci guda baka san meke cikin zuciyar yaro/yarinyar ka ba, don matuqar mutum yakai munzalin balaga, ji yake ya kammala, daidai ma yake da mahaifin sa. Nan zuciyar sa zata fara raya masa abubuwa na banza da wofi mu samman in akai rashin sa'a wajen tarbiyya, akasarin yara da suke ƴan shekaru da suke ƙarewa da 'Teen-Tenn' ɗin nan, 13,14,15, har zuwa ƙarshe.

Su kuma, wanda Allah ya basu haihuwar ƴaƴa mata, yanzun sun maida ƴaƴayen nasu haja (Kayan sayarwa). Daka fara zuwa wajen yarinya neman auren ta, sai a fara tambaya, nawa ka tara, nawa aka tara maka, waye baban ka, menene sana'ar ka??

Na'am, nemawa ɗiyar ka wajen da zata huta abu ne mai kyau, amma gidan tarbiyya, da wadatar zuci shine gidan da soyayya take bunƙasa ciki har ya zam an watadu da abinda Allah ya bada. wani lokaci, da yawan mutane, sai sunyi aur

e Allah ke buɗe masu kofofin arziƙin su, darajar ciyarwa da suke.

Kowa fafutukar sa shine ya sami abinda zai rufawa kansa asiri, har yaji ya wadatu, domin bawan Allah mai hankali da tunani, in yasan ya aje ɗiyar mutane, tana ƙarƙashin kulawar sa ne, sai yafi ƙoƙarin nemowa. Darajar aikata sunnar Masoyin Allah, Masoyin mu (s.a.w.w) kuma saika ga ya mayar da dukkan wani abu daya taɓa masu albarka.

To, abin tambaya anan, yakai Baban ta/baban shi nawa kuka tara, nawa kuka aje a banki, nawa aka aje muku kafin a baku auren matan da kuka haifi ƴaƴayen ku, kafin a aura muku su??? Wasu ma zaka ga, ladan garma ce aka bashi, yana gona, ko makaranta za'a yo mishi saƙo ya dawo ana son ganin sa a gida, daya dawo sai ace ga matar ka cen an ɗaura muku aure da ita shikenen.

Don haka, kirana ga iyaye, lallai, Mu ababen tambaya ne game da yaran mu, haƙƙi ne mai nauyin gaske aurar dasu a lokacin da ya dace, sauƙi ne Allah ya bamu, domin ya fimu sanin abinda yafi dacewa gare mu. Mu sauke nauyin nan, gudun abinda ka kai ya kawo, kada rashin hakan ya saka Allah yayi fushi damu, ya jarabce mu da abinda zuciyar mu bazata jure ɗauka ba.

Allah ya kiyashe mu fadawa tarkon shaiɗan...

Zamu ci gaba Insha Allah

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post