Ilmin Nafsi (Psychology) Cikin Al-Qurani Kashi Na Biyu (2)





 علم النفس القرآن الكريم

(KASHI NA 2)

Abbagano✍

Koda yaushe tambaya tana yawan zuwa wa mutum acikin kwakwalwar sa, wacce wasu yana iya samun amsa, wasu kuma baya samun amsar su.

Mutum yana tambayar kan sa shin yanayiwu wa ya tsira a duniya da lahira?

Ubangiji yana kiran Waɗan nan da suka aikata ayyukan saɓo da alfasha,sudena cire rai da tunanin ko zasu tsira, domin Allah mai rahama ne,

( قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ *وَأَنِيبُوا إِلَىٰ رَبِّكُمْ وَأَسْلِمُوا لَهُ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ)

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai."
Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba."


KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

ABUBUWAN LURA CIKIN AYOYI BIYUN SAMA.

1- A wannan kira da Allah yayi wa bayin sa da kada su fidda rai daga rahamar Sa, ya kuma baiyana musu cewar duk irin wani laifi ko alfasha da suka aikata to haƙiƙa yana iya goge shi.

2- ya kuma ja musu kunnen (التحذير) da zuwan azaba mutuƙar basu nemi yafiyar saba.

Ayar farko tazo da ƙwadaitar wa, akan kada su fidda rai
لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ

Aya ta biyu kuma tana gargaɗi ne ga wanda Basa neman tuban gun Allah (t)
وَأَسْلِمُوا لَهُ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ

Sannan aya ta gaba data zo ta sauwara mana irin natijar da zamu samu idan muka ƙi komawa da gaggawa gareshi ba.

( وَاتَّبِعُوا أَحْسَنَ مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُم مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ بَغْتَةً وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ )

"Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba."

Maganar farko itama kira tayi don bibiyar abinda Allah yake so nuyi
وَاتَّبِعُوا أَحْسَنَ مَا أُنزِلَ إِلَيْكُم مِّن رَّبِّكُم
Sannan kai tsaye natijar ƙinyin haka tazo ga
مِّن قَبْلِ أَن يَأْتِيَكُمُ الْعَذَابُ بَغْتَةً وَأَنتُمْ لَا تَشْعُرُونَ. a

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post