Hikima kayan mumini ce a koda yaushe..




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KA GANIMCI ABUBUWA 5 KAFIN ZUWAN WASU 5 'DIN

A ko da yaushe Annabi (S.A.W.W)na nuna mana abubuwan da za su amfanar damu a duniyarmu da lahirar mu, kamar dai yadda bai boye mana abinda zai cutar damu a duniyar mu da lahirar mu ba.

Babu wani abu guda (koma bayan Allah)wanda za ka iya cewa shi dawwamamme ne wanda ba ya qarewa ko canzawa ba. Saboda haka rayuwa ta kasance abin lissafi a kullum don yiwa kai hisabi.

Manzon Allah (S.A.W.W)na fadawa Abu Zarr Al-Gifari;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ YAA ABU ZARR, KA GANIMCI ABUBUWA BIYAR KAFIN ZUWAN WASU 5;

QURUCIYARKA KAFIN (zuwan)TSUFARKA,

DA LAFIYARKA KAFIN RASHIN LAFIYARKA (tazo maka),

DA WADATARKA KAFIN TALAUCEWARKA,

DA DAMARKA (your chance)KAFIN SHAGALARKA, 

DA KUMA RAYUWARKA KAFIN MUTUWARKA .‘’

(Biharul-Anwar, J:77, Sh:77)

            NAZARI
           ________

Idan muka nazarci wannan hadisi za mu fahinci cewa lalle Annabi (S.A.W.W)ya gama yi mana komai, ko da ace mun taqaita ne wajen aiki da wannan hadisi, domin matuqar za muyi aiki da shi, to, komai ma zai iya shigowa cikinsa.

Samartaka lokaci ne da zai iya bawa mutum damar yin gwagwarma fiye da kowa, yayin da aka ce tsufa tazo masa ba zai iya ba. Ku dubi irin rawar da Imam Ali (A.S)ya taka fiye da sauran tsofin da ya rayu da su.

Lafiya na baka damar aikata duk wani aiki na alkhairi, yayin da jinya ke hana ka aikata ayyukan ibada masu yawa.

KU KARANTA NAN👇
☞ ͡Ku tambaye ni kafin ku rasa ni Fita Na Ɗaya (1)
☞ ͡Du'a Muqatil| Addu'ar biyan bukata da gaggawa
☞ ͡Wallahi akwai maganin Covid-19 a Najeriya Ku tambayi Zakzaky –Inji Wani Bawan Allah

Dukiya na taka rawa matuqa wajen taimakon addinin Allah, domin duk wani yunqurin addini na tafiya ne tare da wadata. Talauci na hana ka aikata abinda ya zama wajibinka, ballantana taimakon wasu ko addini. Ahlus-Duthur namu babban abin misali ne.

Dama (chance), abu ne mai saurin tafiya mai kuma lattin dawowa. Saboda haka, idan ka sami dama sannan ka sake ta kubuce maka, akwai nadama.

Yanzu da kake halin rayuwa ne ka ke da damar neman lahira, amma idan mutuwa tazo maka ba ka da sauran wata dabara, sai dai kawai ka tarar iya abinda ka aikata.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509 

~16th April, 2020.

KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post