Sayyada Zainabul-Kubrah (Ta karbala)!!!




Daga Ma'asumah Nigerian News Update.

Muna godiya ga Allah da Ya abarkaci rayuwar mu da soyayyar Annabi da Iyalan gidansa ma'abota tsarki da daraja, sannan Ya sanya mu daga cikin masu raya al'amuran su.
Kamar yadda yazo a mafi ingancin ruwaya cewa ranar  biyar 5 ga Jimada Ulaa shine yayi dai-dai da ranar haihuwar Sayyada Zainabul Kubra (s.a), 'yar Imam Aliy da Sayyada Zahra yar Manzon Rahma(s) yar uwa ga Imam Hasan da Husain (a.s).

Girman daraja na Sayyada Zainab ya wuce duk yadda mutane suke zato, duba ga mahaifi da mahaifiyarta da 'yan uwanta, ya isa ya tabbatar mana da cewa Sayyada Zainab ta kai kololuwa wajan girma da daraja a wajan Allah(s.w.t). Yazo a hadisin Manzon Allah yana cewa "Idan ba Aliy da Fadima ba, to babu wanda ya kai ya haifi Sayyada Zainab". Wannan hadisin yana nuna mana tsarki na Sayyada Zainab ta yadda bata fito ba sai ta tsatso mai tsarki.

UMMU MASA'IB : Allah sarki Sayyada Zainab ta fuskanci dukkan bala'o'i da musibu a rayuwarta ta yadda idan ba tsatson Annabi ba to babu wanda zai iya jure bala'o'in data fuskanta a rayuwarta. Kamar yadda muke karantawa a tarihi, dukkan Imamai da masoyansu rayuwarsu ta wanzu ne cikin jarabawowi daban-daban, wadannan jarabawowi na musibu basu tsallake kan Sayyada Zainab ba, hasalima nata sun bam-bamta da na saura, domin kuwa da ace za'a daura wa duwatsun duniya girman bala'in da ta fuskanta da sun zamo narkakku (kura).

A gabanta Annabi Ya yi wafati, baya ga haka a gaban idonta aka yi dukkan cutarwar da akayi ma gidan su bayan wafatin kakanta, har zuwa lokacin da mahaifiyarta ta yi shahada, haka ya sake faruwa aka shahadantar da mahaifinta Imam Aliyu (a.s) duk a gabanta, sai ya kasance yanzu bata da kowa sai yan uwanta(Hasan da Husain), suma din ba a tausaya mata ba aka kashe babban yayanta Imamu Hasan tana kallo, ya rage mata saura Imam Husain.

Tana ji tana gani aka yita ma gidan su dauki dai-dai, har saida ya zamanto bata da kowa sai dan uwanta kwara daya shine Imam Husain(a.s). Duk da haka shima bai tsira daga kiyayyar makiya Addinin Kakansa ba. Kowa yasan tarihin abinda ya faru a Karbala na bala'in da Iyalan gidan Annabi suka fuskanta daga wajan makiya Allah. Dukkan wani cin mutumci da kisan Sahabban Imam Husain da kisan Abul Fdhl Abbas da shi kansa kisan Imam Husain din, duk ya faru ne akan idon Sayyada Zainabul Kubra (a.s), kuma duk da wadannan bala'o'i da musibu da Sayyada Zainab ta fuskanta bai sanyata ta rude ba, sabida tsarkin ruhinta.

Sayyada Zainab ta bar mana dukkan abin koyi a cikin rayuwarta daga tarbiyyar da ta sha daga Kakanta Manzon Rahma da Mahaifanta Imam Aliy da Sayyada Zahra(a.s).

Sayyada Zainab(a.s), ta yi wafatine tana da shaikaru 57 a duniya, a shaikara ta 62 bayan hijiran Annabi(s) A birnin Dimashk. Amincin Allah Ya kara tabbata a gareki Ya mai tsarkin tsatson masu tsarki (Sayyada Zainabul Kubrah (A.s).

- Abbakar Ibraheem Kudan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post