Mahanjojin Da iyaye yakamata Su Mallaka Domin Binciken Wayoyon yar`yaryen su A saukake.


Alhamd Cikin iyawar Allah Mas`Udu dan Masani ya Sake dora Alkalaminsa Daya jima da bacci Saboda Wasu Dalilai inda muke Samun kiraye-kirayen ku da korafin ku akan Wannan Makalar da muke gabatarwa,  insha Allah yau munsake dawo wa,  Karku manta Kafi kuci gaba da Karatu ku  Danna….

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook. 

Akwai wadansu manhajoji da aka yi su musamman domin iyaye akan ‘ya’yansu wanda suke taimakawa iyaye wurin sanin abinda ‘ya’yansu suke ciki game da wayoyin da suke mu’amala da su.


Idan yaron ka ya mallaki wayar komai da ruwanki (smartphone) sannan kuma yana iya samun damar siyan data da zai amfani da ita wurin shiga intanet domin yayi bincike ko kuma sada zumunci a cikin shafuka irin na Facebook ko Twitter ko WhatsApp, wasu iyaye kan ji dadi sosai har da sanar da abokansu irin wasa da wadannan na’urori da suke yi.

Amma iyayen da suke da tsabtacceciyar rayuwa hankalinsu baya kwantawa matukar akwai waya a hannayen ‘ya’yansu, musamman iyayen da suka san cewar wannan sahar ta intanet tana da wani bangare na gurbata tarbiya da kuma bawa yaro samun damar da zai yi karatu ko nazari ballantana ya samu damar hutawa domin yin barci.

Saboda wannan dalilai ya sanya wadansu kamfanoni suka kirkiro manhajoji na musamman wadanda ake kira da suna Parental Apps wanda za a iya amfani da su wurin takaita amfani da waya a hannun yaro koda kuwa yayi nesa da gida, haka iyaye zasu iya sanin wadansu manhajoji yake amfani da su, sannan zasu iya dakatar da kowace irin manhaja ce a cikin wayar, za kuma su iya zaban wadansu manhajoji da yaro ba zai iya sakawa a wayarsa ba.

Ba a manhaja kawai abin ya kare ba, iyaye zasu iya gano ina yaron su yake a yanzu, zasu iya sakawa wayar wurare ko unguwanni da basu yarda yaronsu ya wuce ba, ballantana maganar buga game irin wadannan manhajoji suna iya dakatar da kowane irin game ne yaro ya saka a wayar, haka irin wadannan manhajoji suna iya takaita amfani da intanet kuma su daina aiki a lokacin da iyaye suke son su sa yaransu yin barci.

Duk da akwai irin wadannan manhajoji na kyauta, amma a irin wannan yanayi da tarbiya da lalacewar ta ya yawaita a sahar intanet lallai iyaye na bukatar amfani da manyan manhajoji na siye wanda zasu yi aiki fiye da abin da iyayen su ke yin tsammani.



Zamu kawo muku irin wadannan manhajoji mafi shahara da kuma birgewa duk da na siye ne amma iyaye zasu iya gwada amfani da su na wasu kwanaki idan sun ga sun biya musu bukata sai mutum ya siya. Ba kuma mun zabo su bane don mun sami tallansu, sai dai don taimakawa iyayen da suka mallakawa yaransu wayoyin smartphones.

FAMILYTIME (ANDROID DA IOS)


FamilyTime manhaja ce da ta hada komai, domin tana iya baka damar tsarawa wayar yaronka abin zai samu damar amfani da shi, takaita mishi lokacin amfani da wayar, bibiyar wuraren da yake zuwa da dai makamantansu. Ita manhajar zata iya ba iyaye damar su tsara lokacin da yaro zai rika yin aikin da aka bashi a makaranta yayi a gida wato Homowork haka iyaye zasu iya tsaro lokacin da ake bukatar yaro ya kwanta yayi barci domin ya huta. Haka iyaye zasu iya tsarawa wayar yaran nasu iya lokacin da suke son su rika amfani da wayar dake hannunsu.

Wani abun jin dadi da wannan manhaja ta FamilyTime shine kana iya saka wuraren da baka son yaronka ya je, misali ka ce baka son ya wuce daga unguwa kaza zuwa unguwa kaza, to da zarar yaron ya ketare dokar ka wannan manhajar zata sanar da kai cewa yaron yana wuri kaza. Hakazalika a jikin manhajar akwai tracker wacce zata sanar da kai daidai inda yaron yake koda yayi batar dabo.

Daga cikin abin burgewa na wannan manhajar ta FamilyTime shine zai baka damar dakatar da kowane irin manjace ke cikin wayar yaronka da kuma kin ba wayar damar yaron ya iya saukar da manhajojin da baka so. Kari akan haka iyaye zasu iya tace irin shafukan da yaro zai rika ziyarta a intanet, sannan manhajar za ta iya lura da sakon kar ta kwana da ke shigowa wayar yaronka da kuma irin kiran da ke shigowa wayar.

FamilyTime na kudi ne duk da akwai na kyauta wanda ba dukkan wadannan ayyukan da muka lissafo yake iya yi ba. Amma ga wanda yake son amfani da komai da komai zai iya mallakarsa a kan dalar Amurka $27 domin sanyawa waya guda daya, ko kuma ya biya $69 domin amfani da wayoyi guda biyar.

Domin sauke wannan manhajar dannan link dake kasa

FAMILYTIME

QUSTODIO (ANDROID, IOS, KINDLE, NOOK)



Qustodio manhaja ce mai dadin aiki da saukin fahimta kuma tafi dacewa da iyaye da basu da cikakken lokaci ga yaransu. Tana da banban shafin da zai nuna maka duk abubuwan da suka faru a cikin wayar yaronka. Haka zaka san lokutan da yaronka ya bata wurin amfani da manhajoji kamar Instagram ko Twitter.

Tun daga jikin wannan bangon zaka iya tsara tsawon lokacin da yaron zai yi amfani da wadannan manhajoji da kuma bincikan sakonnin da suke shigo mishi waya, zaka iya dakatar da duk wasu gurbatattun shafuka da dakatar da kowane irin manhaja ta game da wacce iyaye basa so.



Ta wane bangare ita manhajar Qustodio tana da sauki domin mutum zai iya mallakarta a $55 domin sawa wayoyi har guda biyar, duk da akwai na kyautarshi amma ba komai da komai yake iya yi ba.

Domin sauke wannan manhajar dannan link dake kasa

QUSTODIO

ESET PARENTAL CONTROL (ANDROID)


ESET yana da nashi kokarin wurin taimakawa iyaye sawa yaransu idanu da sanin shige da ficensu a waya, sai dai shi domin wayoyin android kawai aka yishi. Na kyautar shi yana ba iyaye damar dakamar ta kowace irin manhaja ce a wayoyin yaransu, takaita lokacin buga games, sannan zai iya bada rahoto dan takaitacce. Amma na kudinsa zai kara da rufe kowance irin shafi ne a intanet, gano inda yaro yake ko ya je, aikawa da iyaye sakwanni, da kuma aiko da cikakken rahoton abin da yaro ke yi da wayar. Wani abu da ESET yake iyayi yi zai iya aikowa da iyayen sako domin ba yaron ya iya ci gaba da amfani da wayar ko ko a’a.

Zaku iya gwada amfani da na kudin kyauta har na kwanaki 30 kafin k biya $30 kowace shekara.

Domin sauke wannan manhajar dannan link dake kasa

ESET

WEB WATCHER (ANDROID DA IOS)


Idan kana son ka rika sani da wa yaronka ke amsa waya, wasu irin sakon sms ne ya goge, wasu irin hotuna ne ya dauka ko ya goge to lallai kana bukatar wannan manhajar ta WEB WATCHER.

Wannan manhajar zata iya baka damar kutsawa cikin manhajojin da suke wayarsu irin su Tinder da WhatsApp da Kik da kuma Viber. Za kuma ka iya tsara lokacin da kake son yaron ya rika amfani da wayar, haka zata iya daukar hoton fuskar wayar  ta aiko maka da shi.

Saboda wannan manhajar tana cikin jerin manhajojin dake yin leken asiri shi yasa ba za a iya samunta a Google Play Store ba. Shi yasa wuri saka tama ana bukatar ka dama ta musamman domin sarrafa wayar sosai. Yana da kyau kayi nazari sasai kafin ka saka wannan manhajar kodayake nasan kudinta ma zai iya dakatar da iyaye surin siyanta tunda kudin yana farawa ne daga $130 duk shekara akan kowace waya.

Domin sauke wannan manhajar dannan link dake kasa

WEB WATCHER

NORTON FAMILY PREMIER (ANDROID DA IOS)


Sunan NORTON ba boyayye ba ne kasancewar ya shahara kan maganar VIRUS, haka shima Norto Family Premier ba a barshi a baya ba, wurin lura da sawa yara idanu wurin sanin abin da suke amfani da shi tare da wayoyinsu, musamman yadda suke mu’amala da shafukan intanet.

Ita wannan manhaja ta Norton Family Premier tana baiwa iyaye damar sarrafawa da shiryawa iyaye hanyoyin da zasu lura da yaransu, wanda ya hada da sanya manhajar ta rika dakatar da yaro shiga shafin da su kansu iyaye basu san cewar yana da hatsari da ga yara ba.

Haka za a iya sa Norton ya rika lura da irin lokacin da yaro yake batawa tare da wayar, haka za a iya kashe wayar yaron a duk lokacin da ake bukatar a kashe ta, ta kuma tashi a daidai lokacin da ake bukatar ta tashi, sannan da wannan manhajar mutum zai iya dakatar da duk wani manhaja da ke cikin wayar da kuma hana saka wacce ba a son ganinta a wayar.

Ana iya mallakar wannan manhaja a $50 ba tare da kayyade adadin wayoyin da za a yi amfani da su ba.


Wannan sune kadan daga ciki manhajojin da zamu kawo muku wanda zasu taimaka wurin sanyawa yaronku idanu wurin amfani da wayoyin smartphone da suke tare da su.

Kuyi Ajiye tambayar ka anan kuma ka tabbatar kayi like Din facebook dinmu domin samun sabbin makalolinmu..

DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook,  kar kumanta kuyi like bayan kun danna


Mas`udu dan masani Shinkafi 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post