Sister's| Hijabi Ne Alamin Mu!!!


@Ma'asumah Nigerian News Update@

Fatima Aliyu Adam

Yau daya ga watan fabreru an ayyana shi a matsayin ranar hijabi ta duniya abune wanda ake yin shi shekara shekara wanda nazma khan ta kirkira a shekara ta 2013 wanda hadafin shine a karfafa ma mata gwiwa wajen sanya hijabi.

Hijabi kalma ce ta larabci wacce take nufin shamaki ko katanga.Abu da yafi shahara shine rufe kai wanda mafi yawancin matan musulmai suke sawa wanda ya wuce nan sai dai rufe jiki gaba daya banda fuska da tafi kan hannu.

Matan musulmai zasu sanya hijabi a gaban duk wani namiji da zasu iya aura.

Dangane da hijabi Allah (T) yana cewa a cikin alqur'ani:
 "Kuma ka gaya wa muminai mata suyi kasa da kallonsu,su tsare tufafinsu kada su nuna adonsu sai abinda ya bayyana( kamar zobe na zinari),su saukar da mayafinsu bisa kirazansu kada kuma su nuna adonsu face ga mazajensu,ko babanninsu,ko babannin mazajensu,ko 'ya'ya yansu,ko yaran mazajensu,ko yan uwansu,ko yaran yan uwansu,ko yaran yan uwansu mata ko matayensu ko abinda hannayen damansu ya mallaka ko bayi maza wadanda akayi ma dandaqa ko yara kanana..." 24:31

Allah madaukakin sarki yace a wata ayar " Ya kai Annabi ka umarci matayenka da yaranka mata da Matan muminai su saukar da lullubinsu haka ne yafi dacewa a sansu ba zaa cutar dasu ba" 33:59.
Ayar tayi magana akan lullubi wanda yake nufin shigar musulunci ga mace ba kawai abinda zai rufe kai,wuya da kirji bane sai dai ya hada abun sanyawa wanda zai kasance mai tsayi mai sako sako,ayar ta nuna manufar shiga haka shine a gane matan musulmai kada kuma a cutar dasu.

Lokacin da alqur'ani ya fara bayyana hijabi,bai zo a matsayin mayafi ko marufin kai ba yazo a muhallin shamaki ne kamar a ayar alqur'ani: "...kuma idan zaku tambaye su(matayen Annabi) wani abu,ku tambayesu ta bayan labule shine mafi tsarki ga zuciyoyinku da zuciyoyinsu..."

Sharuddan hijabin musulunci
-Dole ya rube duk jiki
-Dole ya zama baya nuni ko sharara
-Dole ya zama babu kwalliya
-kada ya zama a matse
-kada ya zama da turare

JAISH SHAHID AHMAD ZAKZAKY ZAINABIYYUN ke taya duk matan musulmin duniya murnar ranar hijabi ta duniya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post