Daga: Bin Haroun Sigau
Wasu bata-gari ko kuma ‘yan daba mabiya addinin Hindutva sun hari limamin wani Masallaci a kasar India - Bata-garin sun yi wa limamin masallacin mai shekaru 54 mugun duka Wasu ‘yan dabar Hindutva sun hari limamin wani masallaci ta hanyar watsa mishi asid. Kamar dai yadda aka sani, akwai wata zanga-zanga da Musulman kasar India ke yi sakamakon banbancin da ake nuna musu tun a watan Disamba na 2019.
A jiya ne kuma jaridar Loveforislamic ta walllafa , inda aka tattauna a kan hargitsi da ke aukuwa tsakanin Musulman kasar India da kuma bata-gari.
limamin mai shekaru 54 ya sha mugun duka a masallacin Shiv Vihar kafin daga bisani a yayyaga kayan shi tare da watsa mishi asid a fuska.
Danna Jan Rubutun nan Domin samun Rubuce-rubucenmu a Facebook Yanzu: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update kayi like bayan ka shiga
Binciken masana ya nuna nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401 Akwai bukatar duk musulman duniya su taya musulman kasar India addu’a a masallatai, salloli da kuma sallolin dare.A kara da neman musu yafiyar Ubangiji a kan zunubbansu. Babu cikakken bayani game da mutuwar mutane 30 da aka samu a birnin New Delhi din.Da yawa dai an ce wadanda suka rasa rayukan nasu mata ne da kananan yara.
Tags:
Labaran Duniya