A kullum muminai cikin samun taimakon Allah suke!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

TUN DAGA DUNIYA TSINUWAR ALLAH KE BIN AZZALUMAI

Alqawari ne na Allah cewa tun daga duniya yana taimakon muminai cikin dukkan al'amransu, kuma ba ya bata ayyukansu a duniya ne ko lahira .

Shi yasa kake gani babu baqin ciki ko qunci tare dasu a duniya , sabanin azzalumai da kullum suke cikin firgici da rashin aminci.

Sai dai kuma wawaye ba su cika ganin wannan taimako na Allah da ke yiwa muminai ba, domin su zahiri kadai suke iya gani banda badini. Ko abu na zahirin ma ba sosai suke fahintarsa ba.

 Su kuma azzalumai sukan ga tamkar sun fi qarfi Allah ne da yake bari suna aikata zalunci , shi yasa za ka ji maganganu na wauta na fitowa daga bakinsu .

KU SAURARA KU JI !

Allah (T )na cewa:

👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼

‘’ LALLE MU ZA MU TAIMAKI MANZANNINMU DA KUMA WADANDA SUKA YI IMANI CIKIN RAYUWAR DUNIYA , DA KUMA RANAR DA SHAIDU KE TSAYAWA .

RANAR DA UZURIN AZZALUMAI BA ZAI AMFANAR DASU BA , KUMA GARE SU AKWAI TSINUWA DA MUMMUNAN GIDA (a lahira ).‘’

(SURATUL-GHAAFIR, AYA TA 51-52).

Saboda haka iya uzurin da azzalumai za su iya kawowa kenan a duniya wawaye kuma su karba musu.

Tabbas, mu muna ganin taimakon Allah tare damu kuma muna godiya gare shi bisa wannan taimako nasa da yake mana.

Mu je zuwa, ranar da ba za a karbi uzurinsu ba nanan tafe.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

08137925034-09039791509

~26 February, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post