A ranar Alhamis 26 ga Jimadas Thani 1441H ne sashen daliban Harkar Musulunci almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke karatu a Jami’o’i hudu daban-daban da ke birnin Tehran, a Kasar Iran suka gabatar da bikin Mauludin Sayyida Fatima Azzahra (SA).
(maasumah.com.ng) A ranar Alhamis 26 ga Jimadas Thani 1441H ne sashen daliban Harkar Musulunci almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke karatu a Jami’o’i hudu daban-daban da ke birnin Tehran, a Kasar Iran suka gabatar da bikin Mauludin Sayyida Fatima Azzahra (SA).
Taron, wanda ya gudana a Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya samu halartar yan uwa maza da mata, yan Nijeriya da ke karatu a Kasar Iran da yan wasu kasashe musamman Iran.
Daga wadanda suka gabatar da jawabi a muhallin Mauludin akwai babbar ‘Yar jaridar nan na PressTV, kuma mai fafutukar kare hakkin Dan Adam, Sister Marzieh Hashemi, wacce ta yi jawabi dangane da “Mace Musulma da kalubalen da take fuskanta a wannan zamanin.”

Tags:
Munasabobi