Amurka Ta Kakabawa Wasu Kasashe Takunkuman Tattalin Arziki Saboda Dangantakarsu Da Iran

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya sanar da cewa, Amurka ta kakabawa wasu cibiyoyi da wasu daidaikun mutane a wasu kasashe saboda dangantakarsu da shirin Iran na makamai masu linzami.
(ABNA24.com) Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya sanar da cewa, Amurka ta kakabawa wasu cibiyoyi da wasu daidaikun mutane a wasu kasashe saboda dangantakarsu da shirin Iran na makamai masu linzami.

A cikin bayanin na sa, wanda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a jiya Talata, Mike Pompeo ya bayyana cewa, sabbin takunkuman na Amurka sun shafi kasashen Rasha, China, Turkiya da kuma Iraki, saboda dangantakar da suke da ita da shirin Iran na makamai masu linzami.

Ya ce wannan matakin ya na karkashin shirin hana Iran mallakar makaman nukiliya ne, wanda Amurka ta fadada shi har ya hada da makaman Iran masu linzami, wadanda suke a matsayin barazana ga kawayen Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

Ko a ranar 20 ga wannan wata na Fabrairu da muke ciki Amurka ta bada sanarwan kakabawa wasu jami’an gwamnatin kasar Iran a majalisar kare kundin tsarin mulkin kasar, inda ta ce mutanen suna da hannu a wajen haramta wa wasu ‘yan takaran tsayawa zaben ‘yan majalisar dokokin kasar wanda aka gudanar a ranar jumma’an da ta gabata, wanda Amurka ta ce hakan take hakkokin da ‘yan kasa suke da shi ne a kasar ta Iran
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post