A yau Talata an kuma, Jami'an tsaro sun sake afkawa almajiran Sheikh Zakzaky masu Muzaharar kiran asaki Sheikh Zakzaky a birnin tarayyar Nigeria Abuja. Almajiran Sheikh Zakzaky da ke cigaba da Muzahara na kullum kullum domin kira ga Gwamnatin Nigeria da ta saki Sheikh Zakzaky damai dakinsa Malama Zeenah,:
Yau ma sun sake fitowa a tsakiyar Abuja kuma Jami'an tsaro sun afka musu da harbi da harsasai masu rai gami da ruwan tiyagas. Muzaharar wacce ta soma gudana daga Otaku Market Jabi Abuja, ta zarce ta kama hanyar Under Bridge na Bega bayan Muzaharar ta wuce Under Bridge na Bega har ma an kammala jawabin rufewa sai ga Tigayas na Jami'an tsaro kan masu Muzahara daga nan kuma harsaisa suka biyo baya, wanda aka dauki tsawon lokaci suna ta'addanci kan masu Muzaharar karshe dai aka watse. Zuwa yanzu hada wannan rahoto babu adadin wayanda Jami'an tsaro suka jikkata ko kamu, kuma muna kan bincikawa. Allah yabi mana kadun zaluncin da ake mana a wannan kasa baki daya. Nan wasu daga cikin Hotunan Muzaharar FreeZakzaky ne data gudana a Abuja.




21/01/2020
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates
Tags:
Labaran Duniya
