MUZAHARAR FREE ZAKZAKY A ABUJA: Jami'an Tsaro Sun Kashe Yan Gari

A lokacin Harbin Da Suke Akan Almajiran Sheikh Zakzaky (H) suka harbe Mutanen Gari. Daga Wakilin Mu --Idishia jos. A ci gaba da gudanar da Muzaharar neman a saki Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky da Mai Dakinsa Malama Zeenah Ibraheen yauma Jami'an tsaron yan Sanda sun afka ma muzaharar inda suka bude wuta kan masu Muzaharar bayan kammalawa, lamarin wanda nan take yayi sanadiyyar Mutuwar mutane biyu masu tafiya gidajensu bayan kammala ayyukansu tare da jikkata wani Dan Kabilar Igbo. Muzaharar wanda aka gudanar a babban kasuwar Otake aka nufi Bagger, bayan kammala Muzaharar ne Jami'an tsaron suka hallara a muhallin suka yi ta luguden wuta, masu muzaharar sun watse inda Jami'an tsaron suka kwashe wadanda suka Harba. Jami'an tsaron sun ci gaba da bin yan uwa da jama'ar gari suna kamawa, wanda har yanzu bamu da adadin wadanda aka Kama, amma dai sun Kama wasu yan Uwan. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post