Tsananin Kishi Ya Sa Shi Halaka Budurwarsa A Bauchi.

Marigayiya Patient. Daga Wakilin Mu --Idishia Jos. Wani abin tashin hankali ya wakana a ranar Juma’a sa’ilin nan da wani saurari mai tsananin kishi da aka bayyanashi da ‘Solomon Peters’ ya soki budurwarsa, Patience Zakkari, har ta hakan ya kai ga mutuwarta sakamakon amsa wayar wani na mijin da ta yi a gabansa, lamarin da yanzu hakan ya sanya ake zarginsa da kisan budurwar da suke soyayya tare. Wakilin kamfanin dillacin labarain (NAN) ya labarto cewar lamarin ya wakana ne da karfe 1:30 na daren ranar a gidan da marigayiyar take zaune da ke unguwar Gwallameji a cikin jihar ta Bauchi. Wani majiya da ya bukaci ya sakake sunanshi, ya shaida cewar marigayiyar ta maida mishi bahasin dukkanin ababen da suka wakana kafin ta kai ga mutuwa. Ya shaida cewar al’umman unguwar duk sun shaidi Solomon na soyayya da marigayiyar wanda kowa ya san soyayyarsu ta yi karfi, ya kara da cewa rashin jituwa ta barke a tsakaninsu ne bayan da ta amsa kiran wayar wani abokinta na miji a tsakar daren da hakan ya fusata saurayinta mai tsananin kishi. “Ta shaida min kafin ta mutu cewar dukkanin ababen da suka faru sun wakana ne da karfe 1:30 na shafiyar ranar Juama’ar da ta gabata. “Ta ce min, ta amsa kiran waya daga wajen wani abokinta (wanda ba soyayya suke yi ba sam) nan take sai saurayinta Solomon kishinsa ya motsa ya shiga kishi da hakan da ta yi, ya fara mata ihu da fada, sannan, ta yi kokarin masa bayani amma sam ya fara birgima da ita na dukanta. “Ta dauko kwalba ta maka masa domin ta kare kanta daga tsananin dukar da yake mata, shi kuma sai ya dauko wuka ya cakka mata a baya Ta fada min cewar ya rasa jini sosai domin jininta ya zuba sosai a kasa kafin daga bisani aka garzaya da ita zuwa karamin asibiti bayan da safiya ta yi inda aka mata dan aiki daga baya aka dawo da ita gida da yammaci, kamar yadda take shaida min yadda lamarin ya wakana. Abun takaici, a lokacin da na ba wajen, jikinta ya kara tsananta an sake kaita asibiti daga baya dai rai yayi halisan,” kamar yadda mai bamu riwayar yake bayanin abin da ya faru. Wata majiyar ma mai suna Mercy Cirfat, ta ce Solomon yana zaune kusa da gidan budurwarsa inda gidaje biyu kacal suka raba gidansu, ya arci na kare bayan da ya aikata aika-aikar. Kakakin ‘yan sandan jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, sai ya shaida cewar sun cafke mai mallakin asibitin a bisa gaza sanar da ‘yan sanda faruwar lamarin. Har ila yau, Datti ya tabbatar da cewar sun cafke wanda ake zargi da kashe budurwar tasa a ranar Lahadi. Ya ce za kuma su gurfanar da Solomon Peters, a gaban kotun kan wanna zargin. Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post