"Menene ya Banbanta mu da Zamanin Imam Khumaini (QS)?"
🇳🇬
MA, asuma Nigeria news update 🇳🇬
👉by sharhabil Usman pandoss
Zamanin ne ya banbanta mu ko kuwa lokacin ne, ko yanayin ne ya zama ya banbanta, ko da'awarce ta banbanta da wadda Jagoranmu yake ma Jagoranci, ko kuwa Jagorancin ne ya zama ya banbanta tsakanin Imam da Jagoranmu, ko kuwa dai almajiran ne suka banbanta da na zamanin Imam Khumaini (QS)?
Wadannan tambayoyin suna da matukar gayen muhimmanci a tsakanin almajiran Shaikh Zakzaky (H), da ace kowannenmu zai tambayi kansa da kansa cewa me ya banbanta shi da almajirin zamanin Imam Khumaini? Da amsoshi sun fito, kuma da yanzu mun wuce wannan marhalar.
Akwai hanyoyi da yawa da idan aka bisu za a samu sauyi mai yawa a fagen tafiya irinta gwagwarmaya, misali a wannan lokacin ya dace ace manyanmu suna karantar da mu karatu na gwagwarmaya, suna mana irshadin dakewa a tafarki na gwagwarmaya, suna karanta mana yadda almajiran Imam suka dake suka turje suka tsaya kyam har nasara tazo masu.
Ya dace ace mun dauki irin wannan salon, muna tafiya akansa gaba daya. Yafi kama da ace karatun gwagwarmaya ake mana mu almajiran Shaikh Zakzaky (H), karfa mu manta cewa almajiran Imam sunfi almajiran Shaikh Zakzaky (H) a wancan lokacin fuskantar kalu balen manyan malamai masu adawa da abinda Imam yake hankoron ya tabbata, amma suka jure suka rufe idanunsu akan duk wata murya wadda ba ta gwagwarmaya bace, suka tsaya kyam akan sauraron me Imam yake da bukata da su? Za su aikata duk tsanani duk wuya komi ta fanjama fanjam, sun sallama masa da dukkan ma'anar sallama rayuwa.
A yanzu ma kamata ya yi manyanmu da wadanda suka san bakin zaren da za su yi magana su shajja'a almajiran Shaikh Zakzaky (H), su dinga kawo tarihin tafiyar Imam da mabiyansa yadda suka sallama masa. Mu tambayi kawukanmu misalin ace mabiyan Imam ne almajiran Shaikh Zakzaky (H) a yanzu a wannan halin da su Jagoranmu suke ciki, wanda suke fuskantar barazana ta kisa da barinsu a wannan hali na rashin lafiya tsawon shekaru, ga kuma harbin bindiga, ga shi kuma sauran yan kwanaki a shiga kirkirarrar kotun kama karya wadda wahabiyawan Saudi Arabiya suka tilasta wadannan azzaluman su kai Jagoranmu su yanke hukunci nan da nan, wane tsammani da mataki muke tunanin mabiyan Imam za su dauka su lizimci aikata wa yanzu a aikace? Allah (T) ya sa mun fahimci hadafin wannan zantukan, Allah (T) ya amfanar da mu.

Tags:
Jawaban Malamai