kwana daya bayan majalisa ta yi kira da a cire shugabannin tsaro buhari ya shiga ganawar sirri


Kwana 1 bayan majalisa ta yi kira da a cire shugabannin tsaro, Buhari ya shiga ganawar sirri da su

A halin yanzu shugaba Buhari yana ganawar sirri da shugabannin tsaron Najeriya.

Taron dai ya samu halartar manyan shugabannin tsaro na Najeriya, babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; shugaban ma’aikata, Abba Kyari; ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi; ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola; da kuma mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno.
Bayan su kuma akwai shugaban tsaro na kasa, Janar Gabriel Olonisakin; shugaban sojojin Najeriya, Laftanal Kanal Tukur Buratai; shugaban sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar; shugaban hukumar ‘yan sanda na kasa, Mohammed Adamu; darakta janar na binciken bayanan sirri, Ahmed Rufa’i Abubakar; da kuma darakta janar na hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Magaji Bichi.
Duk da dai cewar har yanzu ba a san dalilin da ya sanya suka shiga wannan ganawa ba, amma dai an san cewa matsalar tsaro musamman a yankin arewa maso gabashin kasar ita ce muhimmiyar maganar da za ayi a kai.
A ranar Talata ne shugaba Buhari ya nuna mamakin sa akan yadda har yanzu aka kasa kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
A jiya kuma ‘yan majalisar wakilai na tarayya suka yi kira da shugaban kasar ya cire shugabannin tsaron na Najeriya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post