Yau ba Ranar kuka bace, Ranar Cika Alkawari ce,

SHAHADA ITACE BABBAN MATSAYI MAFI GIRMA DA DAUKAKA!

Duk manya manyan bayin Allah da suka samu girman daraja da matsayi har a cikin Annabawa za muga daga cutarwa da zaluncin azzaluman zamaninsu ne, wasu ma da yawa daga cikinsu suncika alkawari.
Manzan'Allah (SAWW) shine yafi kowa matsayi da daraja a duk halitta, tarihi ya tabbatarda Manzan'Allah ma Shahada yayi,, haka nan kuma mafi girman daraja da matsayi bayan Manzan'Allah shine Amiril muminin (AS) shima Shahada yayi.
Hakanan Sayyada Zahra (SA) da ya'yanta Hassan da Hussain (AS) suma duk Shahada sukayi,, sannan sauran A'imma (AS) suma dai duk Shahada sukayi. Babu wani matsayi babba wanda ake zuwa ma Allah (T) dashi kamar Shahada a tafarkin Allah,, duk mumini za ka samu yana guri da kwadayin ace shahada itace karshen rayuwarsa.
Ita kuma Shahada ba ana zaben rana ko lokacinda zata zo bane, aa. Duk lokacinda Allah (T) ya kaddara ma bawansa karshen rayuwarsa to shi dai bawan nan yana kwadayin ace ya cika a Shahidi ne. Yau ne gobe ne, koma yaushe ne, ya zama dai itace karshen rayuwa.

Na tabaji su Jagoranmu (H) suna bada misali da lokacinda aka kashe ma Sayyid Nasrullah Dan'sa,, kamar dai shine nakeji idan ba na manta ba, sai Sayyid yake cewa duk wanda zaizo masa gaisuwa shi baya so, sai dai idan za'a zo tayashi murna ne. Wannan daraja da girma take, mu lura dakyau akan wannan fa.

Ba'a yima bawa Hasadar Shahada, sai dai ayi Gibda,, a waki'ar da akayi dinnan a ranar Lahadi a kofar gidan Jagoranmu Sheikh Zakzaky (H) bayan duk yan'uwa sun fito daga gidan Jagora, to na karshe a cikin yan'uwa wanda naga kamar shine yafito shine Sheikh Shahid Turi,, ya samu wani Dan'uwa yana kuka ankashe wane da wane da wane, sai su Sheikh Turi sukace masa Dan'uwa kadaina kuka, yau ba ranar kuka bace, ranar cika alkawari ce, yace ashe ba mune mukayi alkawari cewa ba zamu taba yadda wani abu yafaru da wannan bawan Allah ba sai idan bayan babu rayuwar mu? Yace lallai yau ba ranar kuka bace,, ya kuma ce Wallahi Tallahi shi ba za'ayi wannan kuskuren dashi ba, saboda haka yan'uwa yau ranar cika alkawari ne kawai, a rabu dashi.

Maganganu nanan dayawa na wannan bawan Allah wanda yayi a wannan wajen, wasu duk a gabana yayi. Bayan haka nan kuma kowa yasan girman matsayin Shahada sai wanda Allah ya zaba shine yakeyi,, ba kara zube bane. Idan muka lura da irin girman zaluncinda akayima Jagoranmu Sheikh Zakzaky (H) na kashe masa ya'yansa duka, sai muga cewa wannan dame yayi kama? A cikin wani Jawabin Shahid Ali Haidar yayi, bayan abinda yafaru dasu na waki'ar QUDS, yayi jawabi a Daru-Rahma na cikar kwana 40,, yake cewa gaskiya shi bai dauka cewa su Yaya Ahmad da Hamid za suyi Shahada yanzu ba, ya dauka cewa akwai wani aiki da zasu yi wanda tana yiwuwa zasu dan kara tsawancin kwana, a ma'anar abinda yake nufi dai, dukda ba kalma da kalma na fada ba yadda yafada duka,, Amma kunga yadda Allah yayi nasa ikon, ya bari duk akayima wannan bawan Allah wannan rubdugu haka, hada ya'yansa 6 wanda yake zahiran kowa na ganin gudumuwa da taimakonda sukema wannan da'awa ta mahaifinsu.

To kunga tana iya yiwuwa mu duk yadda muke kallon wannan al'amarin, ya fa wuce tunaninmu, sannan kuma matsayin girman wannan bawan Allah ba fa kadan bane,, ko mu yan'uwa muna iya cewa wannan waki'ar ta shamma cemu, bamu taba tsammanin haka ba, amma kuma haka Allah ya kaddara mana. Yanada kyau mu kara kaimi da jajircewa da dakewa akan wannan al'amarin, wannan bawan Allah indai ka amsa kiransa to ka shiryama duk wata jarabawa, komi zai iya faruwa dakai, ko wane lokaci kuma, yau ko anjima.

Allah (T) kayi mana taimako, Allah (T) ka saka mana zaluncinda akayi mana, Allah (T) ka kawo mana sanadin fitowar Jagoranmu Sheikh Zakzaky (H) Allah (T) ka nuna mana karshen wadannan bakaken yahudawan wahabiyawan azzaluman, Allah (T) ka'amfanardamu.

—Abba Salisu.
20/07/2018.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post