Sistocin Mu 'Kawa Ne A Garemu !!


____
-
Bin Haroun Sigau Ya rubuta;
Wannan sanannen abu ne da kowa ya sanshi, kuma ya yarda dashi.
-
Cewa su mata 'kawa ne a garemu, dalilin haka yasa duk abinda ake so ajawo hankulan mutane a wannan zamani ake amfani dasu.
-
Inka duba gidan mai, kasuwa, shaguna, da sauran wajen saye-da sayarwa zakaga mafi akasarin ma'aikatan mata ne.
-
Don me zaisa muma Sister's dinmu bazasuyi amfani da wannan damar wajen isar da sakon addini a Social media ba?
-
Wannan abu ne da zai bada haske, wajen aikin media ya zam sister's suna taka rawa gaya.
-
Sabila da inka kula zakaga cewa; duk lokacin da akace ga wata mace tayi sabon account a facebook, bata lokaci kankanj zaka samu cewa friend request sunyi mata yawa.
-
Wanda ba komi ne ya jawo hakan ba, kawai don anga sunan mace, to tunda hakane 'yan uwana mata dama ne tazo muku har gida domin samun sauke nauyin daya rataya akanku, na sauke hakkin addini.
-
Wajen yada shi da kara nusar da mutane halin da ake ciki, na zalunci ne ko kuma na fadakarwa ne game da abinda muka sani amma muke kasa aikatawa (tunatarwa).
-
Domin shifa addini nasiha ne, karka dauka duk abinda Malamanmu suke fada wai ba'a sansu bane, a'ah an sansu, kawai dai shi dan adam yana bukatar koda yaushe ake tunatar dashi ne.
-
Sabila da haka Allah (T) ko wanni zamani saiya tadar da mai kira zuwa ga addininsa domin sauke uzuri gobe kiyama.
-
Fatan 'yan uwa na mata zasu gane nufina a wannan dan karamin rubutu dana yi a matsayina na almajiri.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post