Salman ya Ruwaito Cewa:- Abubakar Umar Da Usman Suna Korafi Kan Kullum Manzo Allah (s) Yana Yabon Ali (as) .



-Manzon Allah ya basu amsa, "Bani ne ke yabon Ali ba, sai dai Allah ne yake yabon sa kuma ya bambanta matsayinsa da sauran mutane. Sun tambayi hujjah Manzon Allah (S) ya ba su amsa, "Idan ba ku yarda da kalmomina ba to, lallai babu masu gaskiya kamar mutanen kogo (Ashabul Kahfi).

-Yanzu, zan tura ku baki daya harda Salman kai shaida akansu, don kuyi sha'awarsu ku gashesu. Mutumin wan da da yardar Allah zai farfaɗo dasu kuma zai samu su amsa gaisuwarsa, shine wanda yafi kowa a cikin mutane.

-Sun yarda da wannan sai Manzon Allah ya ce, "Baza Kafet don Ali' bayan an baza kafet Manzon Allah ya umurce su da su zauna a kai. Ali ya zauna a tsakiya sauran ukun su ka zauna a kusurwoyi uku Salman ya zauna a kusurwa ta huɗu.

-Manzon Allah (S) Ya umurci iska ta ɗauki kafet tare da mutanen dake ciki takai su zuwa ga mutanen kogo (Ashabul Kahfi) ta kuma dawo da su cikin ƙoshin lafiya, Salamn yace kawai sai ga wata tashin iska, ta ɗauke mu zuwa sama bata ajemu ko ina ba sai a bakin kogo.

-Muka sauka daga kan kafet ɗin. Ali yace, "wannan ne kogon kuma ga rubutun, tambayi waɗannan mutanen za su fara shiga ne ko ni in gaba ce su.' Sunce za su riga. Dukkan su su ukun su ka miƙe suka yi addu'a suka ce; "Yaku mutanen kogo! Ku amshi gaisuwar mu.' amma ba'a amsa musu ba.

-Sai Imam Ali Ameerul Mu'mineen yai Addu'a guda biyu ya gaishe da mutanen kogon su ka amsa masa. Imam Ali (As) yai jawabi garesu yana mai cewa; "Gaisuwa gare ku, wadanda suka mutu suna matasa, kun bada gaskiya ga Allah saiya ƙara muku shiriya.'

-A cikin amsar su, mutanen kogon suka ce, "Gasiuwar mu a gareka ya ɗan uwan Manzon Allah, magajin shi, Shugaban amintattu, Allah ya ɗauki alƙawari daga garemu cewa; "Baya ga Manzon Allah(S), zamu ci gaba da zama cikin aminci da biyayya gare ka, Waliyinmu, har zuwa ranar sakamako.

-Bayan nan sai jimllan mutane ukun nan (Sahabbai) su ka durqusa su na roƙon Salman ya ce ba abin da zai iya yi, tun da komi yanzun ba yana aiki da umurnin sa bane. Sai su ka roƙi Ali Ameerul Mu'mineen ya mayar da su. Ameerul Muvmineen ya ce, "Ya ke Iska! mai damu zuwa ga Manzon Allah (S).

-Sai ga iska kamar ta farko tazo, ta ɗaga kafet tare da mu ciki. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga mu gaban Manzon Allah (S) wanda shi da kan sa ya ba mu labarin dukkan abin da ya faru yana cewa, Jibreel ya sanar da ni duk abin da ya faru a kogon. Sai dukkan su su ukun suka ce; "Yanzun mun shaida Ali shi ya fi kowa cikin dukkan al'umma."

Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad.............

-Don ƙarin bayani a duba, Irshad Al-Quloub, Shafi na 268.
Ko Littafin, Tara'if, Shafi na 183.

┈┅❀Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ❀┉┈

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post