Sayyadah fateemah Daga Bakin Imam Ali (a.s)


-Muhammad Magaji Katsina

Daga Shafin....
*Ma'sumah Nigerian News Update


1..ME YASA AKA SAWA FADIMA (AS) SUNA FADIMA???

Imam Ali (AS) yace naji Manzon Allah (SAWA) yana cewa ni na ambaceta FADIMA ne saboda Allah (T) ya 'yantata tare da zuriyarta daga shiga wuta duk Mutumin da ya hadu da Allah daga cikin bayi yana mai kadaita shi da Imani da abinda nazo dashi... Aduba Biharul anwar j:34 s:18, Amali Dusy Majalisi na 22 hadisi 5 s:570.
Imam Ali (AS) A wani wajen Yaci gaba da cewa abin sani kawai shine an ambaceta FADIMA (AS) saboda Allah ya 'yantata daga shiga wuta.. Aduba Bisharatul Musdafa S:131 Kashful yakin S:352 Biharul anwar J:43 S:16 ,

2... SHIN FADIMA (AS) HURIL' IYNI CE DA SURAR MUTANE???
Imam Ali (AS) yace naji Manzon (SAWA) yace hakika FADIMA (AS) hurul 'iyn ce da surar mutane.
Aduba Kashful gumma J:1 S:476, Biharul Anwar J:43 S:7 ,

3...SHIN WA MANZO (SAWA) YASANYA A BAYANSA RANAR MUBAHALA???
Imamu Ali (AS) yace lokacin da manyan Kiristocin Najran sukazo wajen MANZON ALLAH (SAWA) shuwagabannin su suka gabato su mutum ukku cikin su akwai Akib da Kays da kuma Askf Sai sukaje wajen Yahudawa alokacin Yahudawan na dakin bautarsu Sai suka kwalla musu kira suna cewa yaku 'yayan Aladu da biririka wannan Mutumin fa suna nufin Manzo (SAWA),
gashi a tsakkiyar ku kuma yana neman yai rinjaye ku sakko muje mu kure shi Sai wani da ake cewa Ibni suriya ya sakko tare da wani Wai shi Ka' abu bn ashraf Sai Kiristocin suka ce dasu kuzo gobe muje mu tuhume shi, to daman Manzo (SAWA) ya saba kullum idan akai sallar Asubah Sai ya zauna yace ko akwai wanda yake da wata tuhuma? Idan ansamu Sai ya amsa masa idon ba'asamu ba Sai ya karantawa Sahabbai abinda akasaukar masa cikin wan nan dare,

To da akai Sallar Asubah Sai Yahudawan nan sukazo suka zauna a gabansa Sai Askaf yace da shi ya baban Kasim wanene baban Annabi Musa? (AS) Sai Manzo (SAWA) yace Imrana ne Sai ya sake cewa to Annabi Yusuf shi kuma waye Babansa? Sai manzo (SAWA) yace Annabi Yakub (AS) ne Sai ya sake cewa kai kuma uwata da ubana su zama fansa agare ka waye Babanka? Sai yace Abdullahi (AS), to shi kuma Annabi Isah (AS) waye Babansa? Sai Manzo (SAWA) ya danyi shuru kadan Sai ga Jibril (AS) Daga sama ta bakwai ya sauko Sai yace masa shi Isah (AS) Ruhine daga Allah ,

kuma Kalmar sa ce Sai Askaf yace to antaba yin Ruhi ba gangar jiki? Sai Allah yayi wa Manzo (SAWA) wahayi da cewa - misalin Isah a wajen Allah kamar misalin Adamu ne an halicce shi daga tirbaya Sai akace dashi zamo Sai yazamo, Ali Imran 59-,
Sai Askaf yayi jayayya yana cewa ta yaya za'ace Isah daga kasa akahalicce shi? Sai yace Muhammad mu bamu samu wan nan a cikin Attaura ko linjila ko Zabura ba Sai a wajenka muka taba jin wan nan maganar to Sai Allah ta'alah ya saukar da ayar Mubahala - ,

Sai yace masa kuzo ku kira 'yayanmu da' yayanku da Matanmu da matanku da kawunanmu da kawukanku Ali Imran aya ta 61- ,

Sai sukace Baban Kasim wace ranar ce ta Alqawarin? Sai yace musu gobe ne insha Allah, suko Yahudawan Sai suka juya suna cewa ba ruwanmu bamuda wata damuwa duk wanda Allah ya halaka a cikin su Kiristocin ko Musulmi,

Sai Imam Ali (AS) yaci gaba da cewa washe gari bayan an gabatar da salla Sai Manzo (AS) ya kama hannuna ya sani a gabansa Sai yakama hannun FADIMA (As) yasata a bayansa ya kuma kama hannunawan Hassan da Husain yasa daya adamarsa daya a haggunsa yana mai samusu albarka
Lokacin da suka gansa a haka Sai sukayi nadama suna me cewa wlh Annabin ne wan nan Mutumin idan muka sake mukayi wan nan Mubahalar tare da ahlinmu to wlh Allah zai Amsa masa addu'ar sa yazamto ya halakamu ba wanda zai tsira gada cikin mu Sai suka rinqa baya a bayan itatuwa har dai sukazo a gaban Manzon (SAWA)
suna cewa ya Baban Kasim saurara mana Sai yace na rantse da wanda ya aikoni da gaskiya da kunzo da ahlinku da Allah baibar wani banasare ko bayahude a doron kasa ba face ya halaka shi.
Aduba munakib na Ibni asub,J:3 S:369, Biharul anwar, J:21 S:348 , tafsirul iya shi j:1 S:177, Tafsirul firatil ufy S:87, Shawahidul tanzy j:1 S:164.

*Mu hadu
a kashi
na biyu (2)
insha Allah.*
Ma'asumiya Nigerian News Updates

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post